Shehu Sani ya lissafa muhimman dalilai 5 da ke janyo rashin tsaro a Najeriya

Shehu Sani ya lissafa muhimman dalilai 5 da ke janyo rashin tsaro a Najeriya

- Shehu Sani ya yi tsokaci kan kallubalen rashin tsaro da ake fama da shi a kasar inda ya lisaffa dalilai biyar

- Ya ce dalilai biyar din ne manyan abubuwan da ke haifar da rashin tsaro a Najeriya

- Sanatan ya ce rashin tattaunawa tsakanin mutane da rashin yaki da rashawa suna daga cikin dalilan

Sanata Shehu Sani ya lissafa dalilai biyar da ke asassa rashin tsaro a Najeriya duk da cewa an kwashe kimanin shekaru goma ana kokarin magance matsalar.

Kamar yadda ya lissafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a 19 ga watan Yuli, Sani ya ce yaki da ta'addanci, sayar da makamai a duniya suna daga cikin dalilan.

DUBA WANNAN: Da dumi-dumi: Atiku da PDP sun kammala gabatarwa kotu shaidunsu 62

Ga cikaken dalilai biyar da sanatan ya bayar:

1 - Rashawa wurin yaki da rashawa

2 - Rashin tattaunawa tsakanin al'umma

3 - Jefa siyasa cikin harkar tsaro

4 - Yadda ake jifa siyasa wurin sayarwa Najeriya makamai

5 - Tallafin da kungiyoyin ta'addan Najeriya ke samu daga kasashen ketare

Idan ba a manta ba Legit.ng ta ruwaito cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun yi wa wata mota dauke da ma'aikatan Action Against Hunger kwantar bauna a hanyarsu ta zuwa Damasak a jihar Borno.

Shashwat Saraf, shugaban kungiyar a Najeriya ya ce harin ya afku ne a ranar Alhamis 18 ga watan July.

Ya ce: "A ranar Alhamis 18 ga watan Yuli sun kaiwa tawagar motoccin mu hari a Damasak a jihar Borno a Najeriya. An kashe direban guda daya, yayin da ma'aikatan kungiyar da sauran direbobin biyu da ma'aikatan lafiya uku kuma ba a gansu ba."

Saraf ya bayyana damuwarsu kan afkuwar harin inda ya ce za suyi kokarin gano mutanen da suka bace domin sada su da iyalansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel