AFCON 2019: Dan wasan Najeriya ya kafa tarihi irin ta Rashidi Yekini

AFCON 2019: Dan wasan Najeriya ya kafa tarihi irin ta Rashidi Yekini

Odion Jude Ighalo ya yi nasarar lashe kyautar takalmin gwal da dan wasa da ya fi kowa zura kwallo a gasar cin kofin kasashen Afirka (AFCON) ta 2019 da aka kammala a daren Juma'a kasar Egypt.

Fittacen dan wasan na Super Eagles ya zura kwallaye biyar a gasar da kasashen Afirka suka fafata da juna.

Ighalo ya zama dan wasan Super Eagles na biyu da ya lashe kyautar bayan tsohon dan wasan Najeriya Rashidi Yekini da ya taba cin kyautar da golden boot.

DUBA WANNAN: Tsohon gwamnan APC ya mayarwa Obasanjo martani kan wasikarsa ga Buhari

Dan wasan na kungiyar wasar kwallo ta Shanghai Shenhua a China ya ci kwallonsa na biyar ne a wasar neman matsayi na uku da Najeriya ta buga da Tunisia a daren Laraba.

Baki daya ya zura kwallaye biyar a wasan.

Ya ci kwallonsa ta farko ne a AFCON a wasar da Najeriya tayi da Burundi. Ya kuma sake zura wasu kwallayen a wasar da Najeriya tayi da Kamaru inda aka tashi 3 -2.

Ya zura kwallonsa ta hudu a raga yayin da Najeriya ta sha kaye hannun Algeria a wasar kusa da na karshe da aka tashi 2 - 1.

Ighalo ya ci kwallonsa ta biyar a wasar cin matsayi na uku da Najeriya ta buga da Tunisia inda ya doke wanda ke biye da shi a baya, Adam Ounsas na Algeria da Sadio Mane na Senegal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164