Bernard Arnault ya doke Bill Gates daga rukunin Attajiri na 2 a Duniya

Bernard Arnault ya doke Bill Gates daga rukunin Attajiri na 2 a Duniya

Bill Gates ya sauka daga matsayin da ya ke kai na mutum na 2 da ya fi kowa kudi a Duniya. Gates ya rasa wannan matsayi ne wajen shugaban kamfanin nan na LVMH watau Bernard Arnault.

Kamar yadda mu ka samu labari daga rahotannin da Bloomberg ta fitar kwanan nan na Attajiran Duniya, Bernard Arnault ne ya dare kan kujerar mutum na 2 a Duniya wanda ya fi kowa kudi.

Wannan Bawan Allah da ya ke tasowa yanzu a Duniyar masu kudi ya sha gaban Bill Gates ne a cikin shekarar 2019 bayan da abin da ya mallaka a ban kasa ya tashi zuwa fam dala biliyan 107.6.

Bill Gates wanda ba sabon shiga ba ne cikin masu kudin Duniya ya koma na uku a yanzu. Har ila yau kuwa, Jeff Bezos shi ne na farko a cikin jerin masu kudin da ke taka kafa a ban kasa a yanzu.

KU KARANTA: Manyan Mawakan Duniya sun tika rawa da rausaya a kasar Saudi

Dukiyar Bernard Arnault ta dara ta Bill Gates ne da Dala miliyan 200 rak. Wannan ya sa mai kamfanin na LVMH ya tsere masa. Arnault Mutumin Faransa ne wanda ya ke kasuwancin sutura.

Kamfanin LVMH ne su ke yin gangariyar kayan Louis Vuitton, Celine, Fendi, Moët, Hennessy, Dom Pérignon, da sauransu. A shekarar 1984 Arnault ya soma rika ya tumbatsa a wannan kasuwanci.

Abin da ya sa dukiyar Bill Gates din ta ja baya ko kuma ya rasa matakin da ya ke a bana shi ne irin taimakon jama’a da ya ke yi a kasashen Duniya. Wannan kyauta ta sa wasu ke zarce masa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel