Hankula sun tashi yayin da wani mutumi ya shige cikin injin din jirgin Azman

Hankula sun tashi yayin da wani mutumi ya shige cikin injin din jirgin Azman

Wani mutumi da ake tunanin mahaukaci ne ya shige cikin injin na jirgin Azman a ranar Juma’a, 19 ga watan Yuli a filin sauka da tashin jirage na Murtala Muhammad da nufin a kais hi birnin Accra na kasar Ghana.

Rahotanni sun bayyana cewa mutumin ya shige cikin jirgin ne mai lamba 5NHAI dake kan hanyarta ta zuwa garin Fatakwal, inda aka jiyoshi yana ihun cewa ‘A kai Accra, ina so na je Accra.’

KU KARANTA: Badakalar naira biliyan 1.4: ICPC ta kai samame ofishin babban jami’i a gwamnatin Buhari

Mataimakin babban manajan kamfanin jirgin Azman, Nuraddeen Aliyu ya bayyana cewa sun fi tunanin ta Katanga mutumin ya bi ya haura cikin filin har ya samu daman shigewa cikin injin din jirgin.

“A lokacin da matukin jirgin ya hangeshi a saman inji a daidai lokacin da jirgin zai tashi, sai ya yi maza maza ya kashe injin din, sa’annan ya sanar da jami’an filin jirgin, jim kadan sai jami’an tsaron filin suka kamashi.” Inji shi.

Ita ma manajan hulda da jama’a ta hukumar jiragen sama na Najeriya, FAAN, Henrietta Yakubu ta tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai tace tuni aka mikashi ga jami’an tsaro don daukan matakin daya dace da shi.

Wata daga cikin fasinjojin dake cikin jirgin ta bayyana bacin ranta game da aukuwar lamarin a shafinta na kafar sadarwar zamani ta Instagram, inda tace “Kusan mintuna 30 jirgin ya tsaya cak a filin jirgi na MMIA, saboda wani mutumi da ya shiga ciki.

“Hankulanmu sun tashi matuka, kuma jami’an tsaro basu isa wurin da jirgin yake ba, ku taimaka ku watsa wannan labarin har sai wadanda abin ya shafa sun gani don su kawo mana dauki.” Inji ta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel