Tika rawa yafi satar kudin talakawa - Adeleke ya mayarwa Gwamna Oyetola

Tika rawa yafi satar kudin talakawa - Adeleke ya mayarwa Gwamna Oyetola

Sanata Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP ya mayar da martani kan kalaman da Gwamna Gboyega Oyetola na jihar Osun ya yi na cewa yana jin kunyar cewa ya yi takarar zaben gwamna da 'dan nanaye'.

A baya, Legit.ng ta kawo muku cewa gwamnan na jihar Osun yayin tarbar shugabannin jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) karkashin jagorancin Yemi Farounbi a ranar 17 ga watan Yuli ya ce bai kamata a bari Adeleke ya yi takara ba tun farko.

A yayin da ya ke martani kan kalamen da aka ce Gwamna Oyetola ya furta, Ademola Adeleke ya ce rawa ya fi satar dukiyar al'umma musamman idan ana rawan ne domin yi wa Allah godiya.

DUBA WANNAN: Na yi wa 'yar ciki na fyade ne domin bata kariya - Mahaifi

Ya kuma yi ikirarin cewa gwamnan na Osun da ya kayar da shi a kotun koli shine ne kan gaba wurin rashawa da rashin basira cikin jerin gwamnonin da suka mulki jihar.

Wani bangare na sanarwar ya ce: "Mutanen Osun sun san cewa ba ni ne aka hada baki da ni wurin sace kudinsu ba. Sama da shekaru takwas, Gboyega Oyetola ne shugaban wadanda ke taimakawa na yi wa mutane sata a karkashin gwamnati mafi muni a tarihin jihar Osun.

"Akwai abinda ya fi sata muni a kasar Yarabawa ne? Ina kallubalantar Oyetola ya fita kan titin Osun idan mutane ba su jefe shi ba. Mutane sun zabi 'dan nanaye' mai gaskiya a maimakon makaryaci da ya jefa su cikin bashi da talauci.

"Mutanen Osun za su tuna cewa bayan kotun koli ta yanke hukuncin ta, na fitar da sanarwar taya Oyetola murna kuma na roki magoya baya na su zaune lafiya."

Adeleke ya cigaba da cewa Oyetola bai tsinana komai ba illa satar kudin al'umma da kuntatawa mutanen Osun a tsawon lokacin da ya yi aiki a matsayin shugaban ma'aikatan gwamna Rauf Aregbesola.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel