Shari’ar Atiku da Buhari: An sha mamaki yayin da shaidan Atiku ya fashe da kuka a kotu

Shari’ar Atiku da Buhari: An sha mamaki yayin da shaidan Atiku ya fashe da kuka a kotu

An sha mamaki a yayin zaman kotun sauraron korafe korafen zaben shugaban kasa na 2019 a lokain da wani shaidan jam’iyyar PDP, da dan takararta Alhaji Atiku Abubakar ya fashe da kuka a gaban kotu yayin da yake amsa tambayoyi daga lauyan shugaban kasa Buhari.

Shaidan mai suna Muhammed Arume Yahaya, wanda shine jami’in tattara sakamakon zabe na jam’iyyar PDP a mazabar Abocho cikin karamar hukumar Dekina ta jahar Kogi ya fashe da kuka ne a lokacin da yake bayanin yadda tashe tashen hankula da aka yi a yayin zaben suka hanashi gudanar da aikinsa.

KU KARANTA: Askarawan Hisbah sun kama mata masu zaman kansu guda 19 a jahar Jigawa

Jaridar Daily Trust ta ruwaito lauyan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Wole Olanipekun ya tambayi Yahaya ko ya san abinda ya faru a akwatin zabe a lokacin da ya tsere don tsira daga harbe harben da yace wasu matasa sun yi? Daga nan ne yasa kuka, inda yace an kashe masa abokai a dalilin harbin.

Da fari dai Yahaya wanda yace mahaifiyarsa ce ta sanya masa suna ‘Honourable’ saboda ya zama babban dan siyasa yace ba’a yi zabe a rumfunan zabe guda 19 cikin 29 dake mazabarsa ba, don haka APC sun hada sakamakon zabe na bogi ne kawai.

Toh amma da lauyan Buhari, Olanipekun, lauyan INEC, Tanimu Inuwa da Lauyan APC, Lateef Fagbemi suka tambayeshi ta yaya ya san haka bayan yace ya boye a lokacin da aka fara harbe harbe? Sai ya basu amsa da cewa iyaka rumfuna 10 kawai ya iya zagayawa kafin a fara harbe harben, don haka bai san abinda ya faru a sauran ba bayan ya tsere.

Haka dai Yahaya ya cigaba da kuka yana zubar da hawaye ana bashi hakuri, da kyar Alkalin kotun, mai sharia Mohammed Garba ya shawo kansa inda ya rarrasheshi yana cewa “Ka daina kuka, mahaifiyarka da ta rada maka suna Honourable so take ka zama mai karfi, don haka ka daina kuka ka amsa tambayoyin.”

Daga nan Yahaya ya cigaba da zayyana ma kotu cewa mazabar Abocho waje ne da PDP keda karfi, da an cigaba da zaben cikin kwanciyar hankali da ta lashe zaben, amma da aka tambayeshi wa ya ci zabe a mazabar a shekarar 2015 sai ya kada baki yace APC.

Bugu da kari, Yahaya yace baya jin Hausa sai yaren Igala, amma lauyoyin APC sun tambayeshi ya aka yi aka sa hannunsa a kan sakamakon zaben da yace da Hausa aka fassara masa, anan ma sai ya kidime yace bai san yadda aka yi haka ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel