Babbar magana: Sai da aka yi mini tayin N360m a kowanne wata idan na shiga kungiyar asiri ta 'Illuminati' - Dr Tumi

Babbar magana: Sai da aka yi mini tayin N360m a kowanne wata idan na shiga kungiyar asiri ta 'Illuminati' - Dr Tumi

- Wani shahararren mawaki na kasar Afirka ta Kudu mai suna Dr Tumi ya bayana cewa an yi mishi tayin wasu makudan kudade

- Dr Tumi ya bayyana cewa an yi masa tayin naira miliyan 360 a kowanne wata, amma idan ya amince zai shiga kungiyar asiri

- Ya ce bayan kudin kuma 'yan kungiyar sunyi masa alkawarin zai yi suna a duniya, kuma zai samu alfarma a duk inda ya shiga a fadin duniyar nan

Wani fitaccen mawaki a kasar Afirka ta Kudu, Tumishang Makweya wanda aka fi sani da Dr TUmi, ya bayyana cewa kwanan nan yayi watsi da wani tayi da aka yi masa na Dala Miliyan Daya wanda ya kai kimanin Naira Miliyan 360 a kowanne wata idan ya yarda cewa zai shiga kungiyar asiri ta 'Illuminati'.

Shahararren mawakin wanda ya fitar da sabon kaset nashi a kasuwa mai suna 'Heart of a King' ya bayyana hakan ne ranar Lahadin nan da ta gabata 14 ga watan Yuli a shafinsa na Facebook.

KU KARANTA: Babbar magana: Babu wanda ya isa ya hana mu yin zanga-zanga a Abuja - In ji 'Yan Shi'a

Makweya ya wallafa rubutun na shi kamar haka:

"Yau da safe sun yi kokarin su jawo ni cikin kungiyarsu ta 'yan asiri. An bayyana mini cewa suna lura dani kuma zanyi amfani matuka. Sun yi mini alkawarin naira miliyan 360 a kowanne wata sannan zanyi suna kuma zan samu alfarma a duk inda na shiga a duniya.

"Amma ni ba irin mutumin da zaku saya da kudi bane. Bazan iya barin ubangiji na saboda kudi ko suna ba. Na riga na gama samun rabo tun lokacin da ubangiji ya busa min rai. Kuma shine zai daga sunana a duniya." In ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel