Wa'iyazubillahi: An kama mai kula da gidan Zoo yayi zina da ta macen gwaggon biri har ya kai ga yi mata ciki

Wa'iyazubillahi: An kama mai kula da gidan Zoo yayi zina da ta macen gwaggon biri har ya kai ga yi mata ciki

- Wani abu da ya faru a kasar Indonesia, ya kawo rudani matuka, yayin da wani mutumi ya yiwa wata ta macen gwaggon biri ciki

- Hakan ya biyo bayan kama wani ma'aikacin gidan zoo da aka yi dumu-dumu da hannu wajen yiwa wata tsohuwar macen gwaggon biri ciki, yayin da wasu kyamarori suka dauki hoton shi a lokacin da yake saduwa da birin

- Mutumin ya bayyana cewa da yardar macen gwaggon birin ya sadu da ita, amma yana neman afuwa saboda bai taba tunanin mutum zai iya yiwa biri ciki ba

Wasu na'urori da aka sanya su a boye sun dauki bidiyon wani mai kula da dabbobin gidan Zoo din yana lalata da wasu daga cikin dabbobin.

"Dabbobi da yawa daga cikinsu sha'awarsu tana tashi idan aka zo basu abinci," in ji Akhiroel Yahya, wanda yake ma'aikacin gidan zoo dinne wanda ya shekara 14 yana aiki.

"Abinda ya samu muka fara zargi shine, yadda muka gano Marylin, tsohuwar ta macen gwaggon birin mu da ciki. Ba ta taba zama tare da wani biri saboda fadan ta, kuma hakan ne ma yasa muka ware mata wajenta daban," in ji shi.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Za a hana kallon fina-finan kasashen waje a Najeriya - Dan majalisa

Wani ma'aikacin gidan zoo din ya bayyana cewa saboda rudewar da suka yi sai da suka dauki mai tsawo kafin suyi bayanin abinda ya faru.

"A farko mun kasa gano ainahin abinda ya faru," in ji daraktan gidan zoo din, Abdoel Hakim.

"Mun gano gaskiyar abinda ya faru ne bayan mun sanya wasu kyamarori a boye a cikin harabar gidan Zoo din."

Haka kuma, da aka tuntubi wanda ake zargin, ya ce duk abinda yayi da macen gwaggon birin sai da suka yi yarjejeniya, ya kara da cewa "Yana kaunar duka dabbobin wajen, amma yana bada hakuri akan cikin da ya yiwa Marylin."

Ya ce bai taba tunanin gwaggon biri zasu dauki ciki da mutum ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel