Sanata Kwankwaso ya tashi ya je Kaduna wajen yi wa Makarfi ta'aziyya

Sanata Kwankwaso ya tashi ya je Kaduna wajen yi wa Makarfi ta'aziyya

Legit.ng ta samu labari cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya kai ziyara zuwa jihar Kaduna domin yi wa tsohon gwamnan jihar ta’aziyyar rashin da ya yi.

Rabi’u Musa Kwankwaso da Tawagarsa sun yi wa Sanata Ahmad Muhammad Makarfi ta’aziyya ne na rashin Mahaifinsa da ya yi a Garin Makarfi a cikin farkon makon idan ba ku manta ba.

Kamar yadda wani daga cikin Hadiman tsohon Sanatan na Kano mai suna Hon. Saifullahi Hassai ya bayyana, Kwankwaso ya isa Makarfi ne da kimanin karfe 5:00 na yammacin Ranar Talata.

Babban ‘Dan siyasar ya yi wa Abokin siyasar na sa gaisuwa tare da addu’a ga Allah ya ba Mahaifin na sa Aljanna. Alhaji Muhammad Na’iya Makarfi ya rasu ne ya na da shekaru 99 a Duniya.

KU KARANTA: An bukaci ganin Ganduje da Abba Gida Gida a gaban Kotu

Kafin rasuwar Marigayin, ya kasance ya na rike da sarautar Majidadin Zazzau. Shi ma dai Mahaifin tsohon gwamna Injiniya Rabiu Kwankwaso shi ne Majidadin kasar Kano a yanzu haka.

A jiya Laraba kuma Sanata Rabiu Kwankwaso ya shiga Garin Kaduna inda ya yi irin wannan gaisuwar ta’aziyya ga Iyalin Abdullahi Umar Mai Rago wanda ya rasu a cikin kwanakin nan.

Kwankwaso ya ziyarci gidan Marigayi Alhaji Abdullahi Mai Rago a gidan na sa da ke kan titin Bima road da ke cikin Unguwar Tudun Nufawa a Birnin Kaduna, inda ya yi wa Mamacin addu’a.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel