Mijina ga sata ga kuma shaye-shaye – Mata ta nemi kotu ta raba auransu

Mijina ga sata ga kuma shaye-shaye – Mata ta nemi kotu ta raba auransu

Wata uwar yara uku, Olubukola Owolabi, a ranar Alhamis, 18 ga watan Yuli, ta shigar da kara wata kotu da ke Ibadan domin a raba auranta da mijinta, Tayo na tsawon shekara 16, kan zarginsa da shan giya da kuma sace-sace.

Olubukola, wacce ta kasance yar kasuwa, tayi zargin cewa Tayo gawurtaccen mashayi ne wanda ke yawan sace mata kayayyakin da take siyarwa.

Tayi zargin cewa a koda yaushe idan Tayo ya shawo giyarsa ya kan ci zarafinta sosai har ya kai ta kusa samun matsalar shanyewar jiki.

Ta bayyana wa kotu cewaridan har mijin nata na so ta ci gaba da zama dashi toh lallai sai sun rubuta sun ajiye cewar zai sauya halayyarsa.

A nashi bangaren, mijin ya ki amincewa da batun rabuwarsu sannan ya amsa dukkanin zargin da take masa.

Tayo, wanda ya kasance ma’aikacin gwamnati ya roki kotu da kada ta raba aurensa da matarsa, sannan ya yi alkawarin sauya halayyarsa.

Alkalin kotun, Alhaji Suleiman Apanda, ya bayyana cewa tunda an riga an shawo kan lamarin, akwai butar ba ma’auratan dammar komawa da alakarsu.

KU KARANTA KUMA: Da zafi-zafi: Shugaba Buhari ya bude taron hukumomin tsaro na sirri na nahiyar Afirka a Abuja

Sai dai kuma ya yi gargadin cewa kotu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen raba auran idan har wanda ake karan ya ki cika alkawarin da ya dauka.

Apanpa ya umurci ma’auratan da su zauna lafiya da junansu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel