Sojoji 6 sun mutu a wani harin bazata da yan ta’adda suka kai masu a Borno

Sojoji 6 sun mutu a wani harin bazata da yan ta’adda suka kai masu a Borno

Yan ta’addan ISWAP sun kashe sojoji shida a wani harin bazata da suka kai a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, wasu majiyoyi na sojoji biyu suka sanar da AFP a ranar Alhamis.

An tattaro cewa mayaka daga kungiyar ISWAP ne suka bude wuta kan wata motar sintiri a ranar Laraba a kusa da Jakana, kilomita 30 daga Maiduguri, babbar birnin jihar, inda suka kashe dukka sojojin da ke ciki.

“Mun rasa dukkanin sojoji guda shida a harin bazata, ciki harda wani kanal.” Inji majiyar farko daga cikin majiyoyin sojin biyu, wanda suka yi Magana bisa sharadin boye sunayensu.

Sojojin na a hanyarsu ta zuwa Maidugui daga Damaturu, babbar birnin jihar Yobe, lokacin da mayakan suka far masu, inji majiyar.

“An lalata motar bindigar da sojojin ke tukawa,” inji majiyar ta biyu.

Biyo bayan harin bazatan mayakan sun kai hari wani sansanin sojoji da ke a wajen Jakana a manyan motoci bakwai dauke da mashin din bindigogi, inda suka dauki tsawon awa guda suna musayar wuta da sojoji, inji majiyoyin.

Sojoji sun dakile harin da maharani suka kai sansanin, inda mayakan ISWAP suka yasar da makamansu da mota daya yayida suka tsere.

KU KARANTA KUMA: Za a fara jigilan Mahajjatan Najeriya daga Madina zuwa Makka a yau

Hare-haren a zuwa ne yan sa’o’i bayan wani Shugaban soji a arewa maso gabas ya gargadi yan ta’adda a yankin da su ajiye makami ko a halaka su.

Zuwa yanzu dai hukumar sojoji bata tabbatar da hare-haren ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel