Yadda masu yankan kai 3 dauke da kawuna 2 suka fada komar Yansanda
Rundunar Yansandan jahar Oyo ta gurfanar da wasu mutane da take zargin yan kan kai ne gaban kuliya manta sabo bayan ta kamasu dauke da kawunan matattun mutane guda biyu a jahar.
Rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito mutanen sun hada da Adekola Martin mai shekaru 45 da Abdullah Basiru mai shekaru 23, da kuma Jimoh Abubakar dan shekara 59, inda rundunar ta tasa keyarsu zuwa gaban kotun majistri dake Iyaganku, Ibadan.
KU KARANTA: Yaki da miyagu: Sojoji sun kashe yan bindiga 145, sun kama wasu 223
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Yansanda suna tuhumar mutanen uku ne da aikata laifuka biyu da suka danganci mallakan kawunan mutane guda biyu ba bisa ka’ida ba, kamar yadda dansanda mai shigar da kara, Sikiru Opaleye ya bayyana ma kotun.
Dansanda Opaleye ya bayyana cewa wasu mutane da a yanzu Yansanda basu kamasu ba tare Martin da Basiru ne suka yanko kawunan, yayin da Abubakar ya amshi kawunan.
“A ranar 11 ga watan Yuli da misalin karfe 3:10 na rana Yansandan dake gudanar da sintiri suka kama Martin da Basiru a kan hanyar Ikoyi zuwa Ile/Ogbomoso dauke da kawunan mutane guda 2 a lokacin da suke kan hanyarsu don kaima Abubakar kawunan.” Inji shi.
Opisa Opaleye yace laifin da ake tuhumar mutanen da aikatawa ya saba ma sashi na 329A da 516 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Oyo na shekarar 2000, don haka ya nemi kotun ta hukuntasu daidai laifinsu.
Sai dai wadanda ake kara su 3 sun musanta aikata laifin, don haka Alkalin Kotun, mai sharia O.Ogunkanmi ya bada belinsu a kan kudi N100,000, tare da mutane biyu da zasu tsaya musu, kowannensu a kan 100,000.
Daga karshe ta dage sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Satumba domin cigaba da shari’ar.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng