Fulani suna da 'yancin zama a kowanne yanki na Najeriya - Yakasai

Fulani suna da 'yancin zama a kowanne yanki na Najeriya - Yakasai

- Tanko Yakasai, Dattijon a Arewa ya soki kirar da kungiyar Northern Elders Forum (NEF) da Coalition of Northern Groups (CNG) su kayi ga Fulani

- NEF da CNG sun shawarci Fulani da ke rayuwa a kudancin Najeriya su dawo arewa saboda rayuwarsu na cikin hatsari

- Yakasai ya ce kudin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 ya bawa dukkan 'yan kasa 'yancin rayuwa a kowanne yanki na kasar

Dattijon Arewa, Tanko Yakasai ya soki kirar da shugabanin kungiyar Northern Elders Forum (NEF) da Coalition of Northern Groups (CNG) su kayi ga Fulani da ke zama a kudancin Najeriya su dawo arewa saboda rayuwarsu na cikin hatsari.

A jawabin da Yakasai ya yi a ranar Laraba 17 ga watan Yuli na rashin nuna amincewarsa da sanarwar da kungiyoyin suka fitar ya ce kudin tsarin mulkin Najeriya ya bawa Fulani 'yancin rayuwa a ko ina a Najeriya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Gobara ta cinye wani sashi na Jami'ar Bayero da ke Kano

Legit.ng ta gano cewa Yakasai ya yi kira ga 'yan arewa da sauran 'yan Najeriya suyi taka tsantsan da mutanen da ba su son hadin kan Najeriya.

Sanarwar ta ce: "Ina son in bayyana rashin amincewa ta da kirar da wasu kungiyoyin arewa su kayi ga Fulani da ke rayuwa a kudancin Najeriya su dawo arewa.

"Ya kamata shugabanin kungiyoyin arewan su sanu cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya bawa dukkan 'yan kasa ikon zama a kowanne yanki na kasar da suka ga dama kuma babu wani mutum ko wata kungiya da za ta iya tauye musu wannan 'yancin."

Yakasai ya ce sashi na 4 na kudin tsarin mulkin Najeriya ya bawa dukkan dan kasan 'yancin zama a duk yankin da ya ke sha'awa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel