Gwamnan jahar Bauchi ya sanar da nadin sabbin mukarrabansa guda 4

Gwamnan jahar Bauchi ya sanar da nadin sabbin mukarrabansa guda 4

Gwamnan jahar Bauchi, Bala Muhammad Kauran Bauchi ya amince da nadin wasu mutane guda hudu mukamin manyan mashawartansa, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito.

Kaakakin gwamnan jahar, Ladan Salihu ne ya sanar da haka a ranar Laraba, 17 ga watan Yuli, inda yace gwamnan ya nada:

KU KARANTA: Zakzaky ya nemi kotu ta bashi daman tafiya kasar India don duba lafiyarsa

- Musa Shittu a matsayin mai bashi shawara a kan harkar siyasa

- Farfesa Sani Malami a matsayin mai bashi shawara na musamman a kan harkokin kungiyoyi masu zaman kansu

- Mohammed Bura a matsayin mai bashi shawara na musamman akan harkokin majalisa

- Abdon Gin a matsayin mai bashi shawara a kan harkokin ayyukan gwamnati.

Sanawar ta kara da cewa Musa Shittu shine tsohon shugaban karamar hukumar Zaki, kuma a yanzu shine shugaban jam’iyyar PDP reshen Arewacin Najeriya. Yayin da Farfesa Malami ya kasance babban likita a asibitin koyarwa ta jami’ar Tafawa Balewa.

Shi kuwa Mohammed Bura, tsohon kwamishinan ruwa ne a gwamnatin tsohon gwamna Isah Yuguda, tsohon sakataren jam’iyyar PDP, kuma shugaban jam’iyyar Green Party of Nigeria na jahar Bauchi mai ci.

Sa’annan kaakakin gwamnan Bauchi ya bayyana cewa Abdon Gin ya taba kasancewa babban sakatare a jahar Bauchi, har ma ya rike mukamin shugaban ma’aikatan jahar Bauchi, daga karshe yace dukkan nade naden sun fara aiki ne nan take.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Gombe, Inuwa Yahaya ya nada Alhaji Abubakar Kari a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jahar Gombe, wanda kafin nadinsa shine daraktan tsare tsare a sakatariyar uwar jam’iyyar APC dake babban birnin tarayya Abuja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel