NDLEA za ta fara farautar manoman tabar wiwi a Jahar Gombe

NDLEA za ta fara farautar manoman tabar wiwi a Jahar Gombe

-Hukumar NDLEA ta shirya yin yaqi da manoma tabar wiwin dake jihar Gombe

-Kwamandan hukumar na jihar Gomben ne ya bada wannan sanarwa ga manema labarai inda ya ce hukumar tasu zata fidda tsari na musamman domin cafke masu aikata wannan ta'asa

-Aliyu Adole yayi kira ga shugabannin gargajiya da malamai kan cewa su fadakar da mabiyansu hadarin shuka wannan taba ta wiwi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA reshen jihar Gombe ta ci alwashin daura qafar wando daya da dukkanin masu noman tabar wiwi a jihar.

Kwamandan hukumar na jihar, Aliyu Adole ne ya bayar da wannan sanarwa ranar Laraba a jihar ta Gombe yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya.

KU KARANTA:Gwamnatin Kaduna za ta rufe makarantun kudi wadanda ba su yin abinda ya dace, inji Kwamishina

Aliyu ya ce, NDLEA za ta shirya domin tsaurara bincike zuwa ko wane lungu da sako a jahar ta yadda za ta samu damar damke masu shuka tabar wiwi.

“ Zamu tsananta bincike kuma duk wanda muka samu da laifi zamu kama shi kana kuma mu gurfanar da shi a gaban shari’a domin ayi masa hukunci.” A cewar Kwamandan.

Adole yayi kira ga wadanda ke niyyar shuka tabar da su yi gaggawar sauya ra’ayinsu zuwa yin shukar wani abin na daban wanda zai amfani rayuwarsu.

Kamar yadda Adole ya ce, hukumar ta kama mutane 14 a shekarar 2017 da kuma wasu 16 a shekarar da ta gabata duk da laifin shuka tabar wiwi.

Kwamandan ya bayyana mana cewa, wasu daga wadanda aka Kaman na jiran a kirasu kotu domin shari’a yayin da wasunsu kuma na gidan yari a garkame.

Aliyu Adole ya kara da cewa: “ Ina so nayi amfani da wannan dama domin yin kira ga wadanda suke makwabtaka da masu shuka gayen tabar da su dauki darasi daga wurin wadanda aka kulle a gidan yari.”

A karshe yayi kira ga shugabannin gargajiya da na addini kan su ja hankalin mabiyansu domin su guji jefa kawunansu cikin harkar noman tabar wiwi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel