An kashe dalibi daga Najeriya a kasar Malaysia

An kashe dalibi daga Najeriya a kasar Malaysia

A na zargin an kashe wani matashi dan kasar Najeriya, Thomas Orhionsefe Ewansiha, mai shekaru 34 a duniya kuma dalibin digiri na uku a jami'ar Limkokwing University of Creative Technology ta kasar Malaysia.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, a na zargin ajali ya yiwa Thomas halin sa yayin da yake tsare a hannun hukumar shige da fice ta kasar Malaysia.

A labarin da 'yan uwan marigayi Thomas suka bayar, hukumar shige da fice ta kasar Malaysia ta tsare shi a ranar 4 ga watan Yulin duk da ya mallaki sahihan takardu na shigowa kasar domin yin karatun digiri na uku.

Jaridar Legit.ng ta samu cewa, Marigayi Thomas ya yi karatun digiri na farko da na biyu a kasar. Sai dai Thomas ya riga mu gidan gaskiya bayan kwanaki biyar da shigar sa hannun hukumar shige da fice ta kasar.

Cikin wata sanarwa da ofishin jakadin Najeriya dake birnin Kualar Lumpur ya gabatar, a na ci gaba da bincike domin gano musabbabin mutuwar dalibin na Najeriya yana tsaka da neman ilimi.

KARANTA KUMA: Buhari ya gana da shugaban bankin ECOWAS a fadar Villa

Shugabar cibiyar kula da harkokin Najeriya a kasashen ketare, Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana bakin cikin ta a kan wannan lamari tare da neman ofishin jakadancin Najeriya dake kasar Malaysia a kan gaggauta samun ba'asi da dalilai na faruwar hakan.

Abike ta jaddada ci gaba da tabbatar da kulawa da jin dadin al'ummar kasar nan a dukkanin inda suka tsinci kawunan su cikin kasashen dake doron kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel