Mutuwa riga: El-Rufai ya jajanta ma Makarfi biyo bayan mutuwar mahaifinsa

Mutuwa riga: El-Rufai ya jajanta ma Makarfi biyo bayan mutuwar mahaifinsa

Gwamnatin jahar Kaduna ta jajanta ma tsohon gwamnan jahar, Sanata Ahmad Muhammad Makarfi biyo bayan mutuwar mahaifinsa, Malam Mohammed Na’iya Makarfi wanda ya rasu a ranar Talata, 16 ga watan Yuli.

Kwamishinan al’amuran cikin gida da harkokin tsaro, Malam Samuel Aruwan ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Laraba dake dauke da sa hannunsa, inda yace gwamnan Kaduna na mika ta’aziyyarsa ga Makarfi, da fatan Allah Ya jikan mahaifinsa.

KU KARANTA: Akasi: kuskuren rubutu ya zaunar da wani mutumi a Kurkuku tsawon shekaru 14

“A madadin gwamnatin jahar Kaduna da jama’an Kaduna gaba daya, Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai na mika ta’aziyyarsa ga tsohon gwamnan Kaduna, Sanata Ahmad Muhammad Makarfi tare da kafatanin iyalan Malam Mohammed Na’iya Makarfi bisa rashin mahaifinsu.

“Marigayi Mohammed Na’iya mutum ne nagari, mai kwatanta jagoranci na gaskiya, kuma ya bauta ma jama’ansa matuka a matsayinsa na basaraken gargajiya. Da fatan Allah ya sanya shi cikin Aljannar Firdausi, Amin.” Inji kwamishina Aruwan.

A wani labarin kuma, Allah Ya kubutar da daraktan kasafi kudi na jahar Zamfara, Hamza Salihu daga hannun miyagu masu garkuwa da mutane bayan ya kwashe kwanaki 2 a hannunsu.

Yan bindigan sun yi awon gaba da Hamza ne a garin Kachia na jahar Kaduna yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa garin Akwangan jahar Nassarawa tare da wasu mutane biyu, sa’annan suka bindige mataimakinsa, Kabiru Ismail da kuma wata budurwa da suka harba a kafa suka barta a kan titi kwance jina jina.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng