Gwamnatin Zamfara za ta dauki matasa 3,800 aiki

Gwamnatin Zamfara za ta dauki matasa 3,800 aiki

-Gwamnatin Zamfara ta kirkiro sabon shirin samawa matasan jihar aikin yi

-Darakatan yada labaran Gwamna Matawalle ne ya bada wannan sanarwa inda yace shirin zai maida hankali ne kan koyar da sana'o'i

-A cewar Daraktan an riga da an kafa kwamiti mai dauke da mutum 9 wanda zai gudanar da wannan muhimmin aiki

Gwamnatin jihar Zamfara a karkashin jagorancin Bello Matawalle ta nada kwamiti na musamman domin daukar matasa 3,800 aiki.

Daraktan yada labaran gwamnan mai suna Yusuf Idris ne ya bada wannan sanarwa ga manema labarai inda ya ce, gwamnati ta kirkiro wani sabon shiri wanda zai samawa matasa hanyar koyan sana’o’i.

KU KARANTA:Gwamnatin Kaduna za ta rufe makarantun kudi wadanda ba su yin abinda ya dace, inji Kwamishina

A cikin wannan sabon shiri za’a dauki matasa goma-goma daga ko wace mazabar dake jihar. Kamar yadda Idris yayi bayani akwai mazabu 114 a kananan hukumomi 14 dake jihar ta Zamfara.

Har ila yau, gwamnatin Zamfara ta riga ta nada kwamiti mai dauke da mutum 9 domin gudanar da wannan shiri na musamman. Usman Dankalili shi ne shugaban kwamitin yayin da Kabiru Mai-Palace zai kasance sakatare.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da; Ibrahim Mahe, Basira Musa, Sa’idu Maishanu, Hussaini Dan-Isa, Oba Obama, Murtala Jangebe da Tukur Limantawa.

A wani labarin mai kama da wannan kuwa, zamu ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ta lashi takobin rufe duk makarantun kudin jihar matuqar basu ba dalibansu ilimi mai inganci.

Kwamishinan ilimin jihar Kaduna, Dr Shehu Makarfi ne ya bada wannan sanarwar ranar Laraba a jihar Kaduna yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN, inda yake cewa, gwamnati za ta fara neman haqiqanin mazaunin makarantun kudin domin cigaba da bibiyar lamuransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel