Daukan aiki: Rundunar sojan ruwa ta saki sunayen yan Najeriyan da suka cancanci shiga aikin Soja

Daukan aiki: Rundunar sojan ruwa ta saki sunayen yan Najeriyan da suka cancanci shiga aikin Soja

Rundunar Sojan ruwa ta fitar da sunayen matasan Najeriya da suka cancanci samun gurbi a cikinta bayan samun nasara da suka yi a jarabawar da suka zana wanda rundunar ta shirya musu na shekarar 2019.

Legit.ng ta ruwaito daraktan watsa labaru na hukumar, Commodore Suleiman Dahun ne ya sanar da haka a ranar Talata, 16 ga watan Yuli, inda ya yi kira ga duk wanda ya zana jarabawar daya duba shafin yanar gizo na rundunar a adireshin www.joinnigeriannavy.com domin duba sunansa.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban karamar hukuma

Daraka Dahun yace rundunar na gayyatar duk wadanda suka ga sunansu zuwa makarantar sakandarin rundunar dake Ojo, jahar Legas don halartar mataki na gaba na daukan aikin, inda zai amsa tambayoyi.

Sanarwar ta kara da cewa ana bukatar duk wanda yaga sunansa ya hallara makarantar daga ranar Litinin, 29 ga watan Yuli zuwa ranar Talata 27 ga watan Agusta, inda za’a tantance takardun karatunsa, a duba lafiyarsa da kuma sake zana wani jarabawa.

Haka zalika ana bukatar duk wanda ya ga sunansa ya taho da abubuwa da suka hada da;

Shaidun kammala karatunsa

Shaidar samun izinin tuki

Alkalami da fensir

Gajerun wanduna 2

Fararen riguna 2

Takalmin gudu

Zanin gado da rigar filo

Cokula/kofi/kwanon cikin abinci

Kanann hotuna guda 4

Daga karshe daraktan yace duk wanda ya tsallake wadannan ranaku da aka sanar, rundunar ba za ta kula shi ba, shikenan ya lashe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel