Da dumi dumi: Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban karamar hukuma

Da dumi dumi: Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban karamar hukuma

Gungun yan bindiga sun yi awon gaba da wwargidar shugaban hukumar karamar hukumar Paikoro na riko, Alhaji Sani Balarabe, Malama Suwaiba Balarabe da nufin yin garkuwa da ita har sai an biya kudin fansa kafin su saketa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito mijinta, Alhaji Sani, yaya ne ga shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jahar Neja, Alhaji Ibrahim Balarabe, rahoton ya kara da cewa an yi garkuwa da Suwaiba ne a ranar Talata, 16 ga watan Yuli.

KU KARANTA: Shari’ar zaben shugaban kasa: Babu abinda ya hada Atiku da kasar Kamaru – Inji Balan gada

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun yi awon gaba da Suwaiba ne tare da wata kawarta, matar manajan wani kamfani mai zaman kansa dake garin Kagara, cikin karamar hukumar Rafi na jahar Neja.

Majiyar ta ruwaito cewa yan bindigan sun kai farmaki cikin garin ne suna ta harbe harbe, inda kai tsaye suka zarce gidan manajan kamfanin, suka yi kokarin tafiya da dansa, amma matarsa ta rokesu su kyale danta su dauketa.

Daga nan kuma sai suka haura katangar gidan shugaban hukumar, jin hakan yasa matar shugaban hukumar ta garkame kanta a cikin bayan gida, amma a dole ta fito bayan yan bindigan sun yi barazanar kashe yan uwanta dake gidan.

Wani majiyar na karkashin kasa ya bayyana cewa yan bindigan sun shaida ma matar cewa mijinta suke nema, amma tunda basu sameshi ba zasu tafi da ita, sa’annan sun nemi a biyasu naira miliyan 100 kafin su saketa.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar, DSP Muhammad Dan-Ina Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma yace suna iya kokarinsu don ceto mutanen da yan bindigan suka yi awon gaba dasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel