Wasikar Obasanjo: Balarabe Musa ya karyata tsohon shugaban kasar

Wasikar Obasanjo: Balarabe Musa ya karyata tsohon shugaban kasar

-Balarabe Musa da Tanko Yakasai sun karyata maganar da Obasanjo ya fadi cikin wasikar da ya rubutawa Shugaba Buhari

-A bangaren guda kuwa zaku ji cewa Ayo Adebanjo da Abdul Usman sun goyi bayan dukkanin abinda tsohon shugaban ya fadi tare da cewa ya kamata a dauki matakin gaggawa a kan ababen da ya lissafo

An samu ra’ayoyi mabambanta daga jiya Litinin zuwa yau da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya rubuta wasika zuwa ga Shugaba Muhammadu Buhari.

Obansanjo a cikin wasikar ta sa ya fadi wasu ababen dake addabar Najeriya inda ya bada karfi a bangaren lamarin tsaro tare da lissafo hanyoyin da za’a iya bi domin magance matsalolin.

KU KARANTA:Ku bar zarginmu da kashe-kashe – Shugaban Fulani

Har ila yau, wannan wasika ta janyo ra’ayin mutane da dama a kasar nan, wadanda daga cikinsu akwai ma’aikatan gwamnati, masana harkokin yau da kullum da kuma manyan ‘yan siyasan Najeriya.

Daga cikin mutanen da su kayi karin haske a kan wasikar, akwai Ayo Adebanjo, shugaban SERAP, Adetokunbo Mumuni da Usman Abdul shugaban Campaign for Democarcy (CD) wadanda suka goyi bayan tsohon shugaban kasan.

Cif Adebanjo a na shi batun ya ce matsalolin tsaron kasar nan sun kai wani matakin da ya kamata a ce an basu kulawa ta gaggawa

A wani bangaren kuwa, tsohon gwamnan jihar Kaduna tun a jamhuriya ta biyu, Alhaji Balarabe Musa da kuma wani gogaggen dan siyasa Tanko Yakasai, sun ce sam maganar Obasanjo bai abin kamawa ba ce..

Balarabe Musa ya ce, tsohon shugaban kasar bai da nagartar fadin gaskiya kan lamuran da kasar nan ke fama da su.

Balarabe Musa ya cigaba da cewa: “ Kowa ya riga ya san Obasanjo burinsa guda daya ne tak, kuma shi ne na ya dai-daita Najeriya. Lokacin da yake rike da mulki mai ya sa bai yi magana a kan haqiqanin abinda ke damun Najeriya ba. Shi ne shugaba mafi muni da muka taba samu a tarihin Najeriya. Bai damu da jama’a ba kamar yadda yake a yau, a don haka Obasanjo ba mutumin da zai fada mana magana bane mun yadda.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel