Zaben Kogi: Duk rigimar da APC take ji ta tareshi ta samu – Inji dan takarar gwamna

Zaben Kogi: Duk rigimar da APC take ji ta tareshi ta samu – Inji dan takarar gwamna

Tsohon gwamnan jahar Kogi dake sake neman kujerar gwamnan a karo na biyu a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Idris Wada ya gargadi jam’iyyar APC da cewa duk rigimar da take ji dashi a wannan zaben gwamnan dake karatowa ta tara ta samu.

Wada ya bayyana haka ne yayin da ya sayi takardar takara daga ofishin uwar jam’iyyar a babban birnin tarayya Abuja, inda yace ba zasu lamunci duk wani tashin hankali a yayin zaben ranar 16 ga watan Nuwamba ba, amma idan APC tace musu kule, zasu ce mata cas.

KU KARANTA: Babban bankin Najeriya ta bayar da lasisi ga wani sabon bankin Musulunci

Tsohon gwamnan yace zasu tara matasa masu karfi a jika, tare da shirya hanyoyin mayar da biki game da duk wata manakisa da tashin hankali da gwamnatin APC mai mulki za ta shirya a yayin zaben gwamnan jahar, domin kuwa za’a yi kare jini biri jini.

“Sun yi amfani da tashe tashen hankula a yayin zaben 2016, amma idan suka sake yin irin haka a zaben nan ba zasu ji dadi ba, domin kuwa a shirye muke, walki muke daidai da gindin kowa, ko kuma ma mu aikata musu abinda yafi nasu.

“Ba zamu zura ido a sace mana zabe ba, zamu yi yaki don kwatar hakkinmu, kuma zamu hada kan yayan jam’iyyarmu, ko a 2016 a kwace mana zabe aka yi, amma saboda Imani da Allah muka hakura, yanzu lokaci ne da jama’a zasu yi karatun ta natsu tare da nazarin ko yau ta fi jiya?” Inji shi.

Daga karshe ya yi alkawarin tabbatar da tsaro a jahar Kogi, sa’annan ya kara da cewa a matsayinsa na tsohon gwamna, zai yi amfani da kwarewarsa wajen gudanar da ingantaccen mulki fiye da yadda ya yi a baya domin amfanin jama’an jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel