Na kwana da dan uwan mijina ne bisa kuskure, na dauka mijina ne - Matar aure

Na kwana da dan uwan mijina ne bisa kuskure, na dauka mijina ne - Matar aure

Wata 'yar kasuwa, Kudirat Ajayi, mai shekaru 52, ta shaidawa wata kotun gargajiya da ke zamanta a yankin Igando da ke jihar Legas cewa ta kwana da surukinta ne bisa tunanin cewa mijinta ne.

Ajayi, mijin Kudirat na tsawon shekaru 35, ya garzaya kotu domin neman ta raba aurensa da matarsa bisa zargin cewa ta na cin amanarsa.

"Ina kwance a kan gado ranar da kanin mijina ya zo gidan da muke haya. Na dauka mijina ne, saboda ya shigo a daidai lokacin da mijina ya saba dawowa gida, karfe 9 xuwa 10 na dare, domin yin mu'amalar aure da ni.

"Sai bayan da ya gama saduwa da ni sannan na gane cewa ba mijina ne, kuma da nayi masa korafi sai ya ce min ya yi hakan ne saboda ya san cewa mijina ya yi bulaguro.

"Da na sanar da matar dan uwana abinda ya faru, sai ta ce na yi shiru da bakina, kar na fada wa kowa, saboda a samu zaman lafiya," a cewar Kudirat

Sai dai, Mista Ajayi, dan kasuwa mai shekaru 71 a duniya, ya shaida wa kotu cewa matarsa mazinaciya ce da ta dade ta na cin amanarsa, lamarin da ya ce ya kai ga har wani daga cikin masu nemanta na ikirarin cewa daya daga cikin 'ya'yansu nasa ne.

DUBA WANNAN: Yadda baki 7 suka mutu a hanyarsu ta dawowa daga daurin aure a Katsina

"Lokacin da na aure ta, na kama mata hayar gida saboda bana son hada ta da ragowar mata na.

"A wurin jama'a na fara jin jita-jita cewa mata ta na cin amanar aurenmu, da farko na yi watsi da maganar kafin daga bisani wani daga cikin samarinta ya tunkare ni da maganar cewa shine uban daya daga cikin yaran da muka haifa.

"Da na tuntubi mata ta a kan maganar sai ta shaida min cewa tabbas mutumin ya taba saduwa da ita amma bai mata ciki ba," a cewar dattijo Ajayi.

Ajayi ya roki kotun ta raba aurensa da Kudirat tare da bayyana cewa bashi da bukatar son cigaba da zama da ita, ya kara da cewa duk son da ya ke mata ya dusashe.

Babban alkalin kotun, Mista Adeniyi Koledoye, ya bukaci ma'auratan su zauna lafiya da juna kafin zuwa ranar 22 ga watan Agusta da kotun za ta cigaba da sauraron karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng