San barka: Mace ta farko a Arewa da ta fara kaiwa mukamin Manjo a hukumar soji

San barka: Mace ta farko a Arewa da ta fara kaiwa mukamin Manjo a hukumar soji

- Manjo Yagana Musa, ita ce mace ta farko da ta fara samun mukamin Manjo a cikin matan kabilar Kanuri

- Yagana ta fito daga garin Gwio-kura dake karamar hukumar Gashua cikin jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya

- Ba kasafai matan arewa suka fiya shiga aikin soja ba dai, sakamakon yadda suke ganin cewa aikin ya sabawa wasu ka'idoji na addini da al'ada

Yagana Musa ta zama mace ta farko a yankin Arewacin Najeriya da ta fara kaiwa mukamin Manjo a hukumar sojin Najeriya.

Yagana ta kasance 'yar kabilar Kanuri ce, wacce shugaban hukumar sojin Najeriya, Laftanal Kanal Tukur Yusuf Buratai ya karramata da wannan mukami.

Manjo Yagana Musa wacce ta samu wannan gagarumin karin girma ta fito daga garin Gwio-kura dake karamar hukumar Gashua, cikin jihar Yobe.

KU KARANTA: Allah ya kyauta: Wajen biki ya koma wajen makoki yayin da wani bam ya tashi ya kashe mutane 6 ciki hadda dan uwan ango

Wannan nasara da Yagana ta samu ya biyo bayan, yadda ba kasafai matan arewa suka fiya shiga aikin hukumar soji ba a Najeriya.

Yanzu haka dai Manjo Yagana Musa ta zama zakaran gwajin dafi a cikin 'yan uwanta mata, domin kuwa ta zarce sa'a ta kuma bar babban tarihi ga yankinta, kabilarta da kuma kasarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel