Allah ya kyauta: Wajen biki ya koma wajen makoki yayin da wani bam ya tashi ya kashe mutane 6 ciki hadda dan uwan ango

Allah ya kyauta: Wajen biki ya koma wajen makoki yayin da wani bam ya tashi ya kashe mutane 6 ciki hadda dan uwan ango

- Kimanin mutane shida ne suka rasa ransu, sannan 14 suka samu muggan raunika sakamakon wani mummunan hari da aka kai wurin wani biki

- A cikin mutane shidan da suka mutu hadda kawun angon, wanda ya halarci shagalin bikin, da kuma wani yaro karami

- An bayyana cewa wanda ya kai harin dama ya gama shirinsa tun safiyar ranar Juma'a, sannan daga baya ya kai harin a daidai lokacin da ake rabawa 'yan biki abinci

Kimanin mutane shida ne suka mutu, yayin da 14 suka jikkata, bayan wani dan kunar bakin wake ya kai wani mummunan hari kan wasu mutane masu taron biki a garin Nangarhar dake kasar Afghanistan.

A cewar wasu hukomomin kasar, mutumin da ya kai harin ya gama shirya bama-baman nashi da safiyar Juma'a a cikin gidan wani babban mai fada aji na kasar.

KU KARANTA: Tirkashi: Ni ba sakaran shugaban majalisa bane, zanyi maganin gwamnatin Buhari - Ahmad Lawan

"Bam din ya tashi a wajen bikin dan uwan Kwamanda Malak Tor, a daidai lokacin da ake bai wa 'yan biki abinci, lokacin da suka gama taruwa a waje guda. A cikin mutane shidan da suka mutu harda shi kansa Tor da kuma wani karamin yaro," a cewar kakakin gwamnan jihar Nangarhar Atahullah Khogyani.

Khogyani ya ce an wuce da mutane 14 zuwa asibiti, inda kuma daga baya ya sake bayyana cewa mutanen da suka ji ciwon sun kai kimanin su arba'in.

Wasu mazauna unguwar da lamarin ya faru a gabansu, sun bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa kimanin mutane 10 ne aka kashe a harin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel