Tirkashi: Ni ba sakaran shugaban majalisa bane, zanyi maganin gwamnatin Buhari - Ahmad Lawan

Tirkashi: Ni ba sakaran shugaban majalisa bane, zanyi maganin gwamnatin Buhari - Ahmad Lawan

- Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya tabbatar da cewa zai yi iya bakin kokarin shi wurin ganin yayi maganin masu kawo matsala a gwamnatin Buhari

- Ya bayyana cewa amma hakan ba zai taba yiwuwa ba har sai sun hade kai sunyi aiki yadda ya kamata

- Ya ce zasu sanya kowanne mutum da yake da mukami a gwamnatin Buhari yayi aikin da aka saka shi yayi

Yau Juma'ar nan ne shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya tabbatar da cewa ba zai zama sakaran shugaban majalisa ba ga gwamnatin shugaba Buhari.

Hakan ya biyo sanarwarr da Mohammed Isa ya fitar, mai taimakawa shugaban majalisar a fannin sadarwa, ya bayyana cewa yaji lokacin da shugaban majalisar dattawan yake fadar haka a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar wasu mata da suka kawo masa ziyara, wadda Joy Emordi, tsohuwar Sanata mai wakiltar Anambra ta gabas ta jagoranci tawagar.

KU KARANTA: Abin da mamaki: Wata mata ta shekara uku tana kwana da gawar mahaifiyarta a daki

"Na yarda da shugaba Buhari a matsayinsa na jajircaccen mutum, sannan kuma na yarda da jam'iyyata, amma na kuma matsalar Najeriya matsalar Najeriya ce, babu wani zancen jam'iyyar APC ko PDP, saboda haka dole sai munyi aiki a tare domin ganin mun kawo karshen matsalar.

"Zamu zamo tsintsiya madaurinki daya a koda yaushe domin ganin mun ciyar da kasarmu gaba. Zamu tashi tsaye domin kalubalantar wani babba da zai kawo mana matsala wurin gabatar da aikin mu. A matsayinka na minista dole kayi aikinka na minista da kyau.

"Zamu sanya mutanen da gwamnati ta basu mukamai suyi aikin da ya kamata. Ba karamin aiki bane, amma dole mu jajirce muyi aiki tare don ganin mun cimma wannan buri namu," in ji Ahmad Lawan

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel