Dandalin Kannywood: Shekaru 12 nayi ina jinya kafin a yanke min kafa, Inji Moda

Dandalin Kannywood: Shekaru 12 nayi ina jinya kafin a yanke min kafa, Inji Moda

Shahararren dan wasan kwaikwayo na Hausa, watau Kannywood, Sani Moda wanda Allah Ya Jarabta da matsalar rashin lafiya har ta kai ga an yanke masa kafa ya bayyana cewa ya kwashe tsawon shekaru 12 yana jinya kafin a kai ga wannan mataki.

Moda ya bayyana haka ne cikin wata hira da ya yi da jaridar Aminiya, inda yace ya dade yana fama da cutar ciwon siga, wanda a baya awon sigan nasa ya kan tashi har ya kai ma’aunin 20, wanda hakan yasa a baya aka taba yi masa aiki aka cire masa yatsu guda biyu.

KU KARANTA: Kwararru kuma amintattu kadai zan nada ministoci a gwamnatina, Inji Buhari

Dandalin Kannywood: Shekaru 12 nayi ina jinya kafin a yanke min kafa, Inji Moda

Sani Moda
Source: Facebook

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Moda yana cewa da fari bayan an cire yatsun sai ya samu sauki, ya koma aikinsa, amma daga bisani jikin ya kara tashi, aka kwantar da shi a asibitin Barau Dikko, daga bisani kuma aka sallameshi, har sai a makon data gabata da aka sake mayar dashi, shine ta kai ga an yanke shawarar yanke masa kafa.

Jarumin ya kara da cewa ya yi fama sosai, wanda har ta kai ga baya iya cin abinci, kuma baya iya zuwa bayan gida sai dai a daga shi, amma cikin ikon Allah a yanzu ya samu sauki fiye da misali, don kuwa awon ma’aunin sigan dake jikinsa baya wuce 6 zuwa 7.

Moda yace: “Na fi kowa murna saboda jarrabawa ce daga Ubangiji babu wanda ya saka min. Kuma babu wanda ya isa ya cire min sai Ubangiji. Kuma daga cikin rukunan imani akwai cewa mutum ya yi imani da kaddara ta sharri ko khairan.

“To, abin da na sani a rayuwa ta duniya shi ne wannan wata lalura ce daga Allah Wanda Shi Ya dora min kuma ban zargi kowa ba. A ranar da aka dawo da ni asibiti sai suka ce abin da ya fi dacewa shi ne a yanke kafar, sai na fi kowa murna kamar ranar da aka ba ni takardar zuwa Aikin Hajji.

“Na ji dadi da farin ciki domin ni na san halin da nake ciki. Kuma wata hanya ce har ila yau da Allah Ya kawo min don samun waraka, ina kuma yin amfani da wannan dama domin yin godiya ga Allah da Ya kara ba ni lafiya.” Inji shi

Daga karshe jarumin ya mika godiya ga masoyansa da suka taimaka masa da kudi da kuma addu’o’i, inda ya yi fatan Allah Ya saka musu da alheri, sa’annan ya gargadi da jama’a dasu kula da masu amfani da sunansa suna karbar kudi wajensu, inda basu ga sunan Sani Idris Kauru ba toh ba nashi bane.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel