Za a biya tsohon gwamnan PDP da ke gidan yari N151.1 a matsayin kudin fansho

Za a biya tsohon gwamnan PDP da ke gidan yari N151.1 a matsayin kudin fansho

- Kotun Ma'aikata na Kasa (NIC) ta umurci gwamnatin jihar Taraba ta biya tsohon gwamnan jihar, Jolly Nyame da wasu mutane uku naira miliyan 151.1

- Kotun ta ce kudin na fansho ne da wasu allawus na tsohon gwamnan da sauran mutane ukun

- Kotun Ma'aikatan ta gargadi gwamnatin cewa rashin biyan kudin a lokacin da ya dace zai janyo karin 10%

Kotun Ma'aikata na Kasa (NIC) ta umurci gwamnatin jihar Taraba ta biya tsohon gwamnan jihar, Rabarand Jolly Nyame da wasu mutane uku naira miliyan 151.1 a matsayin kudin fansho da allawus na watan Mayun 2013 zuwa Oktoban 2015.

Legit.ng ta gano sauran mutane ukun su ne Uba Ahmadu, Abubakar Armayau da Bilkisu Danboyi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ta ruwaito cewa Justice Sanusi Kado ne ya yanke hukuncin bayan lauyan su Uchenna Okeke ya gabatarwa kotu ta karar.

DUBA WANNAN: Jonathan ya roki wata alfarma ta musamman a wurin gwamnatin Buhari

An shiga da karar ne na neman kotu ta tilastawa gwamnatin jihar Taraba biyan tsohon gwamnan da sauran mutane ukun cikin watanni hudu.

Sai dai lauyan gwamnatin jihar Taraba, Emmanuel Anderifun ya nemi ayi watsi da bukatar tsohon gwamnan da sauran mutane ukun inda ya ce Nyame ya dade yana ikirarin cewa yana bin gwamnatin Taraba kudi amma bai gabatar da hujojojin tabbatar da hakan ba.

Sai dai alkalin kotun ya gamsu da hujojin lauyan Nyame ya gabatar inda ya umurci gwamnatin jihar ta biya kudin cikin watanni hudu amma gwamnatin jihar ta ce biya 18 za tayi.

Daga karshe kotun ta amince da biya 10 a kowanne karshen wata inda ta ce rashin biyan zai janyo tarar 10% na jimlar kudin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel