Next level: Tsofaffin Ministoci 12 da zasu koma cikin sabuwar gwamnatin Buhari

Next level: Tsofaffin Ministoci 12 da zasu koma cikin sabuwar gwamnatin Buhari

Wasu sabbin rahotanni dake fitowa sun tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sake mayar da wasu daga cikin tsofaffin ministocinsa mukamansu, ko kuma ya canza musu ma’aikatu a cikin sabuwar gwamnatinsa.

Rahoton jaridar Rariya ya ruwaito akwai yiwuwar mutane 12 daga cikin tsofaffin ministocin Buhari su sake komawa cikin gwamnatin ‘Next Level’ kamar yadda ake yi ma gwamnatin Buharin take, saboda cancanta da kuma rawar da suka taka a baya.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Yan Shia suna gudanar da zanga zanga a garin Kaduna

Daga cikin ministocin da ake Ambato akwai tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami (SAN); Zainab Ahmed (kudi); Hadi Sirika ( Sufurin jirgin sama); Lai Mohammed ( watsa labarai); Aisha Abubakar (harkokin mata); da Babatunde Fashola (ayyuka, gidaje da wutar lantaki).

Sauran sun hada da tsohon ministan ilimi Malam Adamu Adamu; Rotimi Amaechi (sufuri); Mohammed Musa Bello ( Babban birnin tarayya ABuja); Ogbonnaya Onu (kimiyya da fasaha); Solomon Dalung (matasa da wasanni) da Suleiman Adamu Kazaure (albarkatun ruwa).

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kasa ya mika wadannan sunaye ne ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, sai shugaban majalisar bai kai ga bayyana hakan a fili ga takwarorinsa na majalisar dattawan ba.

A wani labari kuma shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa jama’a da dama suna matsa masa lamba game da fitar da sunayen sabbin ministocinsa, sai dai yace ba zai yi gaggawar yin haka ba, saboda a baya ba duka ministocin da ya nada ya sani ba, amma a yanzu so yake sai wanda ya sani zai nada minista.

Buhari ya bayyana haka ne a daren Juma’a, yayin da ya shirya ma yayan majalisar dokokin Najeriya liyafar cin abinci a fadar shugaban kasa, taron daya samu halartar shugaban majalisar dattawa,Sanata Ahmad Lawan da sauran manyan yayan majalisar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel