Mai daki na sai ta bukaci cin hanci kafin na tara da ita - Aboyomi

Mai daki na sai ta bukaci cin hanci kafin na tara da ita - Aboyomi

A gaban kotun al'adu ta majistire dak zaman ta a unguwar Igando ta jihar Legas, wata uwar 'ya'ya hudu, Risikat Adegboyega, ta rasa auren ta bayan kulla sa shekaru 16 da suka gabata yayin da mijin ta, Aboyomi, ya bukaci hakan.

Alkalin kotun, Adeniyi Koledoye, ya salwantar da auren a ranar Alhamis da ta gabata yayin da jaddada wannan hukunci shi kadai ne zai tabbatar da sulhu a tsakanin ma'auratan biyu.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Aboyomi ya shigar da koken sa a gaban kotu na neman sawwake mai dakin sa a sanadiyar tunzura shi wajen neman cin hanci a duk sa'ilin da ya bukaci saduwa da ita.

A yayin zartar da wannan hukunci, Koledoye ya umurci Aboyomi da biya tsohuwar matar sa N200,000 a matsayin kudin rabuwa domin ta ci gaba gudanar da rayuwa wajen tsayuwa da kafafunta a sanadiyar rashin wanda za ta dogara da shi.

KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta nemi babban sufeton 'yan sanda da ya magance annobar fyade a Najeriya

Haka zalika alkalin kotun ya gindaya umarni a kan mai korafin da ya tabbatar da biyan N10,000 a kowane wata domin ci gaba da dawainiya ta rayuwar 'ya'yayen sa biyu masu kananun shekaru.

A makamancin wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, wani matashi mai shekaru 25 a duniya, Lonias Jojo, ya kar mahaifin sa da ya kyamaci auren dake tsakanin sa mai dakin sa, Brende Lube a kasar Zimbabwe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel