An gurfanar 'yar sarkin Makka a kotu saboda dukkan ma'aikacinta

An gurfanar 'yar sarkin Makka a kotu saboda dukkan ma'aikacinta

Mahukunta a kasar Faransa sun gurfanar da 'yar uwar Yariman Saudiyya Muhammad bin Salman a kotu kan tuhumar ta da dukkan wani ma'aikacin da ke mata gyara a gidan ta na alfarma da ke birnin Paris.

Ana tuhumar Gimbiya Hassa bin Salman ne da sanya mai tsaron lafiyarta, Rani Saidi dukkan Ashraf Eid lokacin da aka same shi yana daukan hotunna a gidan ta a shekarar 2016.

Gimbiya Hassa bin Salman 'ya ce ga Sarki Salman bin Abdulaziz.

Duk da cewa Hassa ba ta halarci zaman sauraron karar ba, lauyan ta ya ce ba ta amince da tuhumar da ake mata ba.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Mutum 5 da suka mallaki arzikin da ya fi kasafin kudin Najeriya

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa shaharariyar mawakiyar kasar Amurka Nicki Minaj da ake shirya za tayi casu a binrin Jeddah na kasar Saudiya ta ce ta janye zuwa taron da za ayi a Saudiyya.

Kamar yadda masu mai magana da yawunta ya bayyana, Minaj ta ce ta fasa hallarton taron ne don nuna kin amincewar ta da galazawa 'yan jarida, masu fafutikar neman 'yancin 'yan adam da masu madigo da luwadi da kasar ta Saudiya ke yi.

Minaj ta ce za ta cigaba da amfani da shaharar ta a duniya wurin nemo 'yan cin 'yan adam a fadin duniya.

Kasar Saudiyya dai ta dade tana tsaurarawa kan masu neman 'yancin mata da 'yancin 'yan adam ta hanyar jefa su a kurkuku ko yanke musu wani na'uin hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel