Saurayi ya kashe mahaifinsa saboda ya nemi ya saki matarsa

Saurayi ya kashe mahaifinsa saboda ya nemi ya saki matarsa

Wani matashi dan kasar Zimbabwe mai shekaru 25, Lonias Jojo ya yi amfani da gatari ya yi rotsa kan mahaifinsa mai shekaru 72 sannan ya jefar da gawarsa a wata tsohuwar ramin hakkar ma'adinai saboda ya hana shi auren wacce ya ke kauna.

Anyi ikirarin cewa Jojo ya tsara yadda zai kashe mahaifinsa Luke Robert ne tare da matarsa mai shekaru 18 Brenda Dube da ke zaune a kauyen Village 4 da ke Greenspan Cif Bvute a ranar Alhamisa da ta gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa mamacin baya son surukursa kuma ya dade yana fadawa dansa ya sake ta.

DUBA WANNAN: An kama wasu mata 4 dumu-dumu suna madigo a Kwallejin Kimiyya a Kebbi

Mai magana da yawun mazabar Midlands, Sufeta Goko ya tabbatar da afkuwar lamarin.

"A ranar 4 ga watan Yuli misalin karfe 4 na yamma. Brenda ta dawo gida tatil da giya sannan suka yi cacar baki da Luke wadda daga bisani ya umurci dan sa Lonias ya saki matarsa saboda baya kaunar ta.

"Hakan ya fusata Lonias daga nan sai ya dako gatari ya sari mahaifinsa sau biyu a kansa. Nan take Luke ya fadi matacce," inji shi.

Sufeta Goko ya yi ikirarin cewa mata da mijin ne suka jefar da gawar Luke a cikin ramin hakkar ma'adinai.

"Lonias da matarsa Brenda sun yi amfani da wheel barrow sun dauki gawar mamacin suka jefar a wani ramin masu hakkar ma'adinai mai nisar kilo mita 400 daga gidansu," inji shi.

Ya ce daga bisani Lonias ya shigar da rahoton cewa mahaifinsa ya bata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel