Wata sabuwa: Tarihin da Hausawa ke bayarwa na Bayajidda labarin Gizo da Koki ne - Farfesa Abdallah

Wata sabuwa: Tarihin da Hausawa ke bayarwa na Bayajidda labarin Gizo da Koki ne - Farfesa Abdallah

- Farfesa Abdullahi Uba Adamu, ya bayyana cewa tarihin da Hausawa ke bayarwa na Bayajidda labarin kanzon kurege ne

- Ya bayyana cewa labarin bashi da tushe kwata-kwata a kasar Hausa, ya kuma bayyana wasu garuruwa guda bakwai wanda in dai mutum ba daga cikinsu ya fito ba to ba shi ba Bahaushe bane

- Sannan Farfesan yayi watsi da batun da wasu ke yi na cewa Hausa ba kabila bace yare ne kawai

- Tarihin Bayajidda dai tarihi ne sananne a kasar Hausa, wanda kusan kowanne mutum da ya taso a kasar Hausa ya san da wannan labari

Shugaban budaddiyar jami'ar Najeriya, wacce aka fi sani da NOUN, Farfesa Abdallah Uba Adamu, ya bayyana cewa tarihin da Hausawa suke bayarwa na Bayajidda, labari ne na kanzon kurege bashi da tushe.

Ya kuma bayyana cewa duk Bahaushen da bashi da alaka da wadannan garuruwa guda bakwai da suke yankin arewacin Najeriya, to wannan mutumin ba Bahaushe ba ne. Sai dai za a iya kiranshi da mutum mai magana cikin yaren Hausa.

KU KARANTA: Tsugunne ba ta kare ba: Ku shirya muna nan dawowa gare ku - 'Yan Shi'a sun gargadi jami'an tsaro

Garuruwan da Farfesan ya lissafo sun hada da Katsina, Kano, Daura, Rano, Zaria, Biram da kuma Gobir.

Bayan haka kuma Farfesa Abdallah yayi watsi da batun da wasu masu bincike, manazarta suke fadi na cewa Hausa yare ne kawai ba kabila ba ce, Farfesan ya bayyana cewa Hausawa suna da daulolinsu da jimawa.

Farfesan yayi wannan jawabin ne a lokacin da yaje taron cikar BBC Hausa shekara 60 da kafuwa.

Tarihin Bayajidda, tarihin ne sannane ga ilahirin al'ummar Hausawa, wanda ake koyar dashi a matsayin darasi a wasu makarantu na arewacin kasar nan a sashen Hausa.

Bayajidda a yadda tarihin ya nuna, kusan daga gurin shi Hausa ta samo asali, a lokacin da yaje garin Daura dake jihar Katsina ta arewacin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel