An bani kyautar mota don kar na tona asiri - Wanda ya kashe wasu masoya

An bani kyautar mota don kar na tona asiri - Wanda ya kashe wasu masoya

Rundunar 'Yan sandan reshen jihar Legas sun kama wani Promise Oguegbu mai shekaru 28 bisa laifin kashe wani mutum da masoyiyarsa Ejibo a garin na Legas inda ya ce matar mutumin ne ta shirya yadda za a kashe mijin nata.

An tsinci gawar Rasaki Balogun mai shekaru 56 ne da Muyibat Alabi a ranar 20 ga watan Yunin 2019 a gidansa mai lamba 16 Taiwo Oke Street a rukunin gidajen Victory da ke Ejigbo.

An gano gawarwakinsu ne bayan matar wani Akorede da ke zaune a Iba Estate ta kaiwa 'yan sanda rahoto.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Mutum 5 da suka mallaki arzikin da ya fi kasafin kudin Najeriya

Daga nan ne 'Yan sanda suka fara bincike inda aka gano motar mamacin a jihar Imo hannun wani Promise Oguegbu kuma aka damke shi.

An gano cewa Ogueegbu ya dauke katin ATM din mamamcin inda ya rika cire kudi daga asusun ajiyarsa na banki.

A yayin da 'yan sanda ke holensa, sun ce ya kashe Balogun ne yayin yi masa fashi da makami amma Oguegbu ya musanta hakan.

A cewar wanda ake zargin, matar mutumin da wani mutum ne suka kashe Balogun inda ya ce shi dai an mika masa motar ne domin ya rufa musu asiri.

Ya ce: "Ban kashe kowa ba. Matan mai gidan ne ya kashe mijinta da budurwarsa. Ni kadai na ga lokacin da ta ke aikata hakan. Ta roki in rufa mata asiri hakan kuma ya jefa ni cikin fitina.

"Ya faru ne a ranar 18 ga watan Yunin 2019. Na dawo daga kasar waje ne kuma ina kokarin komowa Korea ta Kudu amma ba a bani biza ba. A gidansu na ke haya."

Oguegbu ya cigaba da cewa matar mamacin ta kira shi ya taya ta aiki amma da ya shiga sai ya tarar da mijinta a daure tare da wani dogon mutum a tsaye inda ta umurci ya daure budurwar mijin kuma ya aikata hakan saboda ya tsira da ransa.

Ya kuma ce ya ga lokacin da ta ke zuba wani abu a bakin mijin da budurwarsa kuma daga bisani ta mika masa motar da ta ce nata ne ta roki ya rufa mata asiri.

Ya ce ba shine ya kashe mutumin da budurwarsa ba sai dai shiru da ya yi ne ya jefa shi cikin matsala.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel