Yawan kisan kai a Najeriya: Sanatoci sun nemi a hana sayar da ‘Sniper’ a kasuwa

Yawan kisan kai a Najeriya: Sanatoci sun nemi a hana sayar da ‘Sniper’ a kasuwa

Majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta haramta hadawa, shigowa, da kuma sayar da fiya fiyan kashe kwari mai suna Sniper a Najeriya, sakamakon ya zama abinda yan Najeriya ke amfani dashi wajen kashe kansu.

Majalisar ta dauki wannan mataki ne a ranar Talata, 9 ga watan Yuli bayan Sanata Theodore Orji na jahar Abia ya gabatar da kudurin haramta sayar da fiya fiyan saboda yadda ya zama annoba a tsakanin matasan Najeriya.

KU KARANTA: Ba kunya ba tsoron Allah: Tsohon gwamnan APC da matarsa sun kwashe motocin naira biliyan 1

Yawan kisan kai a Najeriya: Sanatoci sun nemi a hana sayar da ‘Sniper’ a kasuwa

‘Sniper’
Source: Facebook

Sanatan yace: “Matsalar kashe kai da kai da yan Najeriya suke yi ta hanyar amfani da fiya fiya baya rasa nasaba da halin talauci da suka tsinci kansu a ciki, wasu kuma sun rasa wanda suke kauna ne, rashin lafiya ko kuma batawa tsakanin masoya.

“Amma za’a iya dakatar da matsalar idan har yan uwa da abokan arzikin shi wanda yake shirin kashe kansa suka saurareshi, suka bashi kwarin gwiwa akan matsalar da yake ciki, tare da zama kusa dasu, da kuma kawar da duk wani abu da zasu iya amfani dashi kamar wuka, igiya, kwayoyi, da fiya fiyan sniper.” Inji shi.

Sanata Albert Bassey Akpan na jahar Akwa Ibom ya bukaci sauran Sanatoci dasu sanya wani tsari a mazabunsu na zakulo duk mutanen dake fama da wata muguwar damuwa domin share musu hawayensu, shi kuma Sanata Rochas Okorocha kira ya yi ga gwamnati ta samar da ma’aikatar farin ciki da jin dadi don magance matsalar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel