Ke Duniya: Wallahi ina neman wacce zanyi lalata da ita ne - Abinda wani gardi ya ce kenan yayin da aka kama shi a dakin mata na FCE Kano

Ke Duniya: Wallahi ina neman wacce zanyi lalata da ita ne - Abinda wani gardi ya ce kenan yayin da aka kama shi a dakin mata na FCE Kano

- 'Yan Sanda sunyi nasarar kama wani katon gardi da yayi kokarin shiga cikin hostel din mata dake kwalejin ilimi ta tarayya a jihar Kano

- An kama gardin sanye da kayan mata harda hijabi da likabi, inda ya bayyana cewa yayi hakan ne domin ya badda kama

- Ya bayyana cewa ya samo kayan da yayi amfani dasu ne a dakin kakarsa, amma yana rokon ayi masa afuwar ba zai kara aikata laifi irin wannan ba

Dubun wani katon gardi ta cika yayin da aka kamashi a cikin bangaren dakunan mata na kwalejin ilimi ta tarayya dake Kano, wato FCE Kano.

An kama gardin ne sanye da hijabi da likabi kamar dai yadda mata ke sakawa ya, inda ya bayyana cewa yayi hakan ne domin ya badda kamaninsa, ma'ana yayi basaja ya samu damar yin lalata da wacce tsautsayi ya fada mata.

KU KARANTA: In kasan na fada baka san na mayarwa ba: Duniya ba ta taba yin kasurgumin barawo ba a tarihi irin Abacha - Omokri ga El-Rufai

Matashin yayi bayanin hakan ne yayin da aka yi masa bidiyo, domin jin dalilin da yasa ya aikata wannan abu.

Da aka tambayeshi inda ya samo kayan da ya sanya, ya bayyana cewa: "Na kakarshi ne ya dakko domin yayi amfani da su, amma ya roki jami'an 'yan sandan da suyi masa afuwa akan cewa ba zai kara aikata wannan laifi ba."

Yanzu haka dai matashin yana hannun jami'an 'yan sandan domin cigaba da gabatar da bincike akan shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel