In kasan na fada baka san na mayarwa ba: Duniya ba ta taba yin kasurgumin barawo ba a tarihi irin Abacha - Omokri ga El-Rufai

In kasan na fada baka san na mayarwa ba: Duniya ba ta taba yin kasurgumin barawo ba a tarihi irin Abacha - Omokri ga El-Rufai

- Karshen satin nan da ya gabata ne gwamnan Kaduna El-Rufai ya bayyana cewa matasan arewa suna da gaskiya da rikon amana

- Ya bayyana hakan ne a lokacin da yayi maganar cewa ba a taba kama wani damfarar yanar gizo ba dan arewa, koda yaushe 'yan kudu ake kamawa

- Hakan ne ya tunzura Reno Omokri, inda ya bayyana cewa duniya ba ta taba yin kasurgumin barawo ba a tarihi irin Sani Abacha

Tsohon na hannun daman tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya mayarwa da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai martani akan maganar da yayi na cewa matasan arewa suna da gaskiya da rikon amana.

A karshen satin nan da ya gabata ne, gwamnan Nasir Ahmed El-Rufai ya bayyana cewa ba a taba kama wani matashi dan arewa da laifin damfarar yanar gizo ba, saboda suna da gaskiya a dukkanin lamuransu.

Sai dai kuma, Reno Omokri, a lokacin da yake mayar da martani akan maganar gwamnan, ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar mulkin soja, Janar Sani Abacha wanda yake dan asalin arewa ne, shine babban barawon da duniya ta taba yi a tarihi.

KU KARANTA: Babbar magana: Sarkin Kano ne ya tunzura matan arewa suke kashe mazajensu - Hon. Zulyadaini Sidi Karaye

"Ya kai El-Rufai kafin ka kira 'yan kudu da 'yan damfara, ka sani cewa babban barawon da aka taba yi a tarihin duniya shine Sani Abacha. Amma duk da haka an samu filin wasa a Kano da aka sanya masa sunanshi.

"Wannan shine mutumin da ya sace kudi kimanin dala biliyan 5. Shekara 21 da mutuwarsa kenan amma har yanzu ba a kammala kwakwalo kudin da ya sata ba, duk da dai cewa shugaba Buhari ya ce Abacha bai yi sata ba.

"Babban barawo a tarihin ma'aikatan Najeriya shine Abdulrasheed Maina, wanda Buhari ya bai wa mukami a boye. Barayin kasar nan basu da wata kabila, shekaru 8 da suka wuce, na ce bambancin Najeriya ba tsakanin kudu da arewa bane. bambancin yana tsakanin masu gaskiya da marasa gaskiya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel