Yadda wata kyakyawar budurwa ta mutu ranar auren ta

Yadda wata kyakyawar budurwa ta mutu ranar auren ta

Dangin wata mata malamar makaranta, Peral Sedinam Lulu, sun shiga halin kadu wa da juyayi bayan mutuwar ta a yankin Volta da ke kasar Ghana a ranar da za a daura mata aure.

A ranar juma'a, 5 ga watan Yuli, ne aka shirya gudanar da daurin aure na gargajiya a tsakanin Lulu da Mawufemor Kosi Wampah, saurayin ta da suka dade su na soyayya, sannan ranar Asabar, 6 ga watan Yuli, a daura musu aure a Coci.

Rahotanni sun bayyana cewa Lulu ta yi korafin cewa ta na fama da ciwon kai a ranar Juma'a yayin gudanar shagalin bikin al'ada na aurensu. Ta rasu 'yan sa'a'o'i kadan bayan an garzaya da ita asibiti.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, dan uwa ga Lulu ya ce marigayiyar ta amsa wani kiran waya daga kawar ta kafin ta yi korafi da ciwon kan da ya zama silar mutuwar ta. Sannan ya kara da cewa har yanzu basu san abinda kawar Lulu ta fada mata ba a wayar da suka yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel