Yadda wani dattijo mai shekaru 73 ya angonce da amarya mai shekaru 63 a Zaria

Yadda wani dattijo mai shekaru 73 ya angonce da amarya mai shekaru 63 a Zaria

Wani bikin aure tsakanin wasu dattijai biyu; namiji mai shekaru 73 da wata mata mai shekaru 63, ya jawo cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya ma'abota amfani da dandalin sada zumunta.

A cewar Chinecherem Ebubechi, mutumin da ya fara yada hotunan bikin dattijan a dandalin sada zumunt, ya ce angon, Matthew Owojaiye, mai shekaru 73, ya auri sahibarsa, Abosede Ayobola, mai shekaru 63.

A cewar Chinecherem, ango Matthew, malamin addinin Kirista, ya auri Ayobola ne a karo na farko tun farkon fara soyayyarsu, shekaru 50 da suka wuce.

Ya bayyana cewa bayan haduwarsu ta farko a wancan lokacin, Mathew ya gayyaci Ayobola domin su fita tare amma sai ta ki amincewa da hakan.

Soyayyarsu ta kullu ne bayan sun sake haduwa a karo na biyu bayan wasu shekaru masu yawa. Duk tsawon wannan lokacin babu wanda ya yi aure a tsakaninsu, hakan ne ma ya sa suka yanke shawarar bawa juna dama har so ya kullu a tsakaninsu.

Sun yi aure a Cocin 'Living Faith' da ke garin Zaria a gaban 'yan uwa da abokan arziki'

Yadda wani dattijo mai shekaru 73 ya angonce da amarya mai shekaru 63 a Zaria

Amarya da Ango da abokan arziki
Source: Twitter

Yadda wani dattijo mai shekaru 73 ya angonce da amarya mai shekaru 63 a Zaria

Dattijo mai shekaru 73 ya angonce da amarya mai shekaru 63 a Zaria
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel