Mahaifina zai mutu idan ba'a dau mataki ba - Dan El-Zakzaky

Mahaifina zai mutu idan ba'a dau mataki ba - Dan El-Zakzaky

Haifaffen dan El-Zakzaky, Mohammed Ibraheem Zakzaky ya bayyana damuwarsa kan lafiyar mahaifinsa da kuma tsoron zai iya mutuwa cikin kowani lokaci.

Mohammed ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayinda ya gabatar da jawabi ga manema labarai a Abuja kan lafiyar mahaifinsa, Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Abdullahi Musa, dan kungiyar mabiyan Shi'an ne ya karanta wannan jawabi a madadin Mohammed Ibrahim El-Zakzaky.

Mohammed ya ce yana zargin gwamnatin Najeriya da kokarin hallaka iyayensa da gayya saboda har yanzu ba'a dau mataki ba duk da sakamakon gwajin da likitansu yayi kuma ya bayyanawa gwamnati.

KU KARANTA: Karfin hali ko ganganci: Wani hafsan kwastam ya yi kokarin yiwa Hameed Ali juyin mulki

Yace: "Duk da cewa ban son in fidda rai a yanzu; na ga akwai yiwuwan in ceto rayuwarsu, saboda duk wani matakin da muka dauka bai yi aiki ba."

"Bisa ga abubuwan da na ji daga likitoci a makon da ya gabata, ya zama wajibi in bayyana cewa lokacin da aka bada domin kula da su ya wuce. Yanzu ba ni da wani abinda zan iya yi."

"Abinda ya fi damu na shine na ga ganin wasu alamu a jikinsa kamar irin wanda muka gani a Junairun 2018 da ya samu ciwon Bugun jini."

"Yayinda a lokacin ya na jin zafi a lokaci bayan lokaci, yanzu wannan azaba ya zama kullum."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel