Budurwa ta kashe dan uwanta saboda ya hana su yin fati a Kano

Budurwa ta kashe dan uwanta saboda ya hana su yin fati a Kano

Rahotanni sun kawo cewa wata matashiyar budurwa mai suna Ummi ta kashe dan uwanta da suke uwa daya uba daya sakamakon takaddama da ta shiga tsakaninsu bayan ya hana su yin fati a unguwar Badawa da ke karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa lamarin ya afku ne a yammacin ranar Asabar, 6 ga watan Yuli a daidai lokain da ake tsaka da shagalin bikin yar’uwarsu.

Jaridar ta tattaro daga majiya mai tushe cewa bikin wata kanwarsu akeyi sannan kuma cewa a jiya Juma’a akayi fati sannan kuma yauma kamar yadda aka tsara za’ayi a kofar gidansu, Sai mamacin, mai suna Malam Sani, Wanda malamin makarantar Islamiyya ne yace baza’ayi fatin ba yayinda ita kuma Ummi, wadda ake zarginta da kashe dan uwan nata tace dole sai sunyi abinsu.

Suna cikin tsaka da cacar baki ne sai ta bude baki ta zagi Malam Sani, wanda ya kasance Dan uwanta kuma yayanta, shi kuma nan take ya dauki hannu ya mare ta.

Majiyar ta kara da cewa bayan ya mare ta ne kuma sai ta tafi cikin gida shine ya biyo ta nan take kuma ta dauki wuka ta caka masa a wuya inda a nan take yace ga garinku nan.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin da ke kin shirin Ruga na so a ci gaba da rikici – Miyetti Allah

Tuni dai aka binne Malam Sani kamar yadda addinin musulunci ya tsara yayinda ita kuma Ummi aka mika ta hannun hukumar ‘yan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel