An kama wasu mata 4 dumu-dumu suna madigo a Kwallejin Kimiyya a Kebbi

An kama wasu mata 4 dumu-dumu suna madigo a Kwallejin Kimiyya a Kebbi

Kwallejin Kimiyya da Fasaha na Jihar Kebbi da ke Jega ta kori wasu dalibanta mata hudu saboda samunsu da aikata laifin madigo.

Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban makarantar da aka yi wa karin daraja, Aminu Dakingari, ya ce jami'an tsaro da masu sharar dakunnan kwanan matan ne suka kama 'yan matan yayin da suka aikata madigon.

Ya ce an kafa kwamitin ladabtarwa wadda ta gudanar da bincike kan lamarin kuma ta gano daliban sun aikata laifin kana daga bisani aka kore su daga makarantar.

DUBA WANNAN: Kannywood: Adam Zango ya nuna sabuwar babbar mota ta miliyan N23m da ya saya

"Daliban sun fadawa kwamitin binciken cewa sun aikata laifin saboda haka ya zama dole mu kore su daga makarantar," inji shi.

Ya kara da cewa daliban sun rika masa barazana bayan an kore su daga makarantar, "Sun rika barazanar halaka ni ta hanyar sakon tes amma hukumomin tsaro sun shiga tsakanin mu," a cewar shugaban makarantar.

Ya kara bayani inda ya ce biyu daga cikin daliban da aka kora 'yan garin Kontagora ne a jihar Neja yayin da sauran biyu sun fito ne daga jihohin Kebbi da Sokoto.

Madigo da luwadi dai manyan laifuka na a dokar Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel