Jerin sunayen jihohi da kananan hukumomin da za su iya fadawa matsalar amai da zawo a kasar nan

Jerin sunayen jihohi da kananan hukumomin da za su iya fadawa matsalar amai da zawo a kasar nan

Rahotanni sun kawo cewa hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta jero wasu jihohi da kananan hukumomin kasar da cutar amai da gudawa zai addaba idan ba a dauki mataki ba.

Hukumar ta gano haka ne a bincike da ta kaddamar da tare hadin guiwar ‘eHealthAfrica’ inda ta bayyana cewa jihohin Kano, Kebbi da Sokoto na cikin wadanda za su yi fama da wannan matsala idan ba ayi gaggawan daukan mataki a kai ba.

NCDC ta ce sakamakon wannan binciken zai taimaka wajen fadakar da gwamnatocin jihohin kasar nan wajen maida hankali game da cutar.

KU KARANTA KUMA: An kama matasa 3 da suka yi wa yar shekara 14 fyade a lokaci guda a jihar Niger

Ga jerin jihohin da kananan hukumomin a kasa:

1. Jihar Kano – Wudil, Kiru, Gwarzo, Karaye, Shanono, Bagwai, Kabo, Rimin Gado, Tofa, Madobi, Gaya, Dawakin Kudu, Fagge, Ungogo, Bichi, Dawakin Tofa, Tudun Wada, Garun Malam, Bebeji, Rano, Bunkure, Kibiya, Doguwa, Gezawa, Rogo, Kumbotso, Kura

2. Jihar Kebbi – Aleiro, Argungu, Gwandu, Augie, Maiyama, Suru, Koko-Besse, Dandi, Birnin-Kebbi, Jega, Kalgo, Bunza, Ngaski, Yauri, Shanga

3. Jihar Sokoto – Tambuwal, Bodinga, Binji, Yabo, Sokoto South, Wamakko, Dange, Shuni, Sokoto North, Kware, Silame, Kebbe, Shagari, Tureta, Rabah

4. Jihar Borno– Jere, Monguno, Biu, Kwaya, Kusar, Bayo, Hawul, Damboa, Askira/Uba, Dikwa, Mobbar

5. Jihar Zamfara– Gusau, Bakura, Gummi, Bukkuyum, Anka, Maru, Talata, Mafara, Maradun, Birinin, Magaji-Kiyaw, Zurmi

6. Jihar Kaduna– Igabbi, Zaria, Kaduna south, Soba, Ikara, Kudan, Makarfi, Sabon Gari, Kauru, Kubau

7. Jihar Bauchi– Bauchi, Jama’are, Dass, Bogoro, Tafawa -Balewa

8. Jihar Nasarawa – Akwanga, Toto, Obi

9. Jihar Yobe – Gujba da Gulani

10. Jihar Kwara – Ilorin west da Ilorin East

11. Jihar Niger – Agwara da Magama

12. Jihar Kastina–Danja

13. Jihar Taraba – Ibi

14. Jihar River– Andoni

15. Jihar Plateau– Jos North

16. Jihar Benue – Markurdi

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel