Ra’ayi Riga: Gwamnatin Gombe ta ce babu wanda ya isa ya hana ‘Ruga’ a Gombe

Ra’ayi Riga: Gwamnatin Gombe ta ce babu wanda ya isa ya hana ‘Ruga’ a Gombe

-Gwamnan Gombe ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta samar da wuraren zama na Ruga

-Gwamnan ya bayyana haka ne bayan da ya gama ganawa da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa

-Ya bayyana rashin jin dadinsa game da dakatar da shirin samar da Ruga da gwamnatin tarayya tayi

Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya bayyana rashin jin dadinshi game da dakakatar da shirin samar da wajajen zama na Ruga da gwamnatin tarayya tayi, inda ya bayyana cewa jihar Gombe za ta kaddamar da shirin samar da wajajen zaman.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yau Juma’a 5 ga watan Yuli 2019 bayan da ya gama ganawa da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa dake a Abuja.

A ranar Laraba 3 ga watan Yuli 2019, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta dakatar da shirin samar da wajajen zama na Ruga da ma’aikatar aikin noma ta gwamnatin tarayya ta kirkira a matsayin daya daga cikin hanyoyin inganta harkar kiwo a Najeriya.

KARANTA WANNAN: Ai ga irinta nan: An daure Ahmed tsawon watanni saboda yada hotunan batsa

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ne ya bayyana matsayar gwamnatin tarayya bayan da kwamitin magance fada tsakanin makiyaya da manoma na zauren tattalin arzikin kasa (NEC) da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ke jagoranta suka gama ganawa a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Umahi ya bayyana cewa shirin inganta harkar kiwo tsari ne na kowa da kowa. Duk jihar da ke da bukata, to za ta iya shiga cikin tsarin.

Amma gwamnan jihar Gombe wanda yayi magana da Hausa, ya bayyana cewa “Shirin shugaba Buhari na samar da Ruga shiri ne mai kyau, kuma jihar Gombe, wanda mafi yawancinsu Fulani ne za su tabbatar da shirin.”

Ya kara da cewa “Yanzu haka da nike magana da ku, gwamnatin Gombe ta ware fili sama da hekta 200,000 don samar da wajajen zama na Ruga.”

“Saboda wasu jihohi sun ki amincewa da shirin bai zama dole a ce itama Gombe ba za ta iya yi ba. Har yanzu bani so in yarda cewa an dakatar da shirin. Mu za mu cigaba da shirin saboda tsari ne mai kyau da zai magance matsalolin da mutanen mu (Makiyaya) ke fuskanta.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa an dawo da aikin madatsar ruwa na Dadin Kowa inda ya bayyana cewa yanzu ana tura ruwa da ya kai yawan lita miliyan 40 a duk rana don anfanin yau da kullun a jihar Gombe.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel