Ministocin Buhari: Abin da yasa har yanzu aka ji shiru – Faruk Adamu Aliyu

Ministocin Buhari: Abin da yasa har yanzu aka ji shiru – Faruk Adamu Aliyu

Guda daga cikin makusanta, kuma na hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari, Faruk Adamu Aliyu dan mutan Birnin kudu na jahar Jigawa ya bayyana dalilin da yasa Buhari ke jan kafa wajen zaben sabbin ministocinsa.

Alhaji Faruk ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar Aminiya, inda ya danganta jinkirin da shugaban kasa Buhari ke yi wajen nada ministoci ga gudun sake fada ma kura kuran daya tafka a baya wajen zaben tsofaffin ministocinsa a farkon hawansa.

KU KARANTA: Wata Mata ta yi ma mijinta dukan tsiya har sai daya fadi matacce a Kano

A cewar Faruk, an samu korafe korafe game da wasu kura kurai da aka tafka a tafiyar gwamnatin shugaba Buhari a baya, hakan tasa a yanzu ake tuntubar jama’a da dama da suka bada gudunmuwa ga nasarar cin zabe domin kauce ma irin wancan matsala.

“Akwai korafi kan kura-kurai da aka yi kan yadda tafiyar ta kasance a baya, sakamakon haka ake ta tuntubar juna a tsakanin bangarori mabanbanta da ake ganin sun taimaka wajen sake samun nasarar zaben, ba ana cewa za a iya gamsar da kowa ba ne, amma ana ganin hakan zai rage korafin da ya faru a baya.” Inji shi.

A wani labarin kuma, hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta kammala tantance akalla mutane 21 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika mata don tantancewa tare da gudanar da bincike akansu kafin ya mika sunayensu ga majalisa a matsayin wadanda yake muradin nadawa mukamin ministoci.

Wata majiya ta karkashin kasa daga fadar shugaban kasa ta shaida ma majiyar Legit.ng cewa DSS ta kammala binciken mutane 21, kuma ta amince dasu, sa’annan tace a asirce ake gudanar da binciken don gudun kada a siyasantar da lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel