An gano yarjejeniyar da aka kula tsakanin Goje da Shugaba Buhari kafin ya janye takararsa

An gano yarjejeniyar da aka kula tsakanin Goje da Shugaba Buhari kafin ya janye takararsa

- An dakatar da shari'ar da ake yi wa Sanata Danjuma Goje na tuhumarsa da satar kudi naira bilyan biyar

- Rahotanni sun bayyana cewa Attorney Janar na kasa ne ya bayar da umurnin watsi da shari'ar bisa umurin Shugaba Muhammadu Buhari

- An bayyana cewa anyi yarjejeniya da Goje ya janye takararsa na shugabancin Majalisa yayin da shi kuma za ayi watsi da tuhumar da ake masa a kotu

Babban Kotun Tarayya da ke zamanta a Jos tayi watsi da shari'ar da ake yi kan Sanata Danjuma Goje bisa umurnin Attoney Janar na kasa, Abubakar Malami da aka ce Shugaba Muhammmadu Buhari ne ya bayar da umurnin aikata hakan.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa an yi wata yarjejeniya da Shugaba Muhammadu Buhari inda aka bukaci Goje ya hakura da takarar shugabancin majalisa domin bawa dan lelen Buhari, Ahmed Lawan daman lashe zabe yayin da shi kuma za a bukaci EFCC tayi watsi da tuhumar da ake masa.

DUBA WANNAN: Kannywood: Adam Zango ya nuna sabuwar babbar mota ta miliyan N23m da ya saya

Ana zargin Goje ne da sace kudi har naira biliyan 5 tsakanin watan Satumba zuwa Nuwamban 2010 bayan ya yi kirkiri wata takardar bogi ne neman ciyo bashi mai lamba GM/HA/RES/VOL. 1/17.

An bayar da umurnin watsi da karar ne bayan Malami ya bawa alkalin da ke sauraron shari'ar umurnin aikata hakan a yayin zaman kotun da aka gudanar misalin karfe 6 na yammacin ranar Alhamis.

A zaman kotun da aka gudanar cikin gaggawa, wani Niyi Akintola (SAN) ne ya wakilci Goje yayin da wani Paul Asika daga Ma'aikatar Shari'a ya gabatar da takardar.

Hakan na nufin za ayi watsi da shari'ar bisa umurnin Attoney Janar na kasa, Abubakar Malami.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel