Allah sarki: Dan Allah ku fito ku aureni, wallahi rashin miji ne ya hanani yin aure - Jaruma Maryam Yahaya

Allah sarki: Dan Allah ku fito ku aureni, wallahi rashin miji ne ya hanani yin aure - Jaruma Maryam Yahaya

- Jaruma Maryam Yahaya ta bayyana cewa, rashin mijin aure ne ya saka har yanzu take yin harkar fim

- Ta ce komai lokaci ne da aure da mutuwa duka na Allah ne, saboda haka idan lokacinta yayi dole zata yi

- Ta bayyana irin nasarorin da ta samu a harkar ta fim da kuma wani babban kalubale da ta fuskanta a lokacin da take shirin fara harkar fim

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausan nan wacce tauraruwar ta ke haskawa a yanzu, Maryam Yahaya ta bayyana dalilin da ya hanata yin aure a yanzu.

Jarumar ta bayyana hakan ne a wata hira da tayi da gidan rediyon Freedom dake Kano, inda ta ce: "Aure da mutuwa duk lokaci ne na Allah, idan lokacina yayi zan yi dole, yanzu babu mijine, ku fito ku aure ni, rashin miji ne ya hanani yin aure, kowa yasan maza na wahala yanzu."

KU KARANTA: Babbar magana: Matar wani alkali a Gombe ta kashe yaron alkalin a kan idonsa

Jarumar ta bayyana cewa ta samu nasarori masu yawan gaske a sana'ar da take yi ta wasan kwaikwayo, kuma ita babu abinda zata ce da wannan sana'a tata sai dai tayi godiya ga Allah.

Maryam ta bayyana wani babban kalubale da ta fuskanta, inda ta bayyana cewa da farko iyayenta sun ki amincewa ta shiga wasan Hausa fim din, yayin da ita kuma take matukar son shiga harkar.

Amma daga baya da fitaccen jarumin wasan Hausa Ali Nuhu yaje ya zauna da mahaifinta yayi masa bayani ya kyaleta akan taje ta fara wasan Hausan.

Kwanakin baya jarumar ta bayyana cewa tana matukar so taga ta fito a matsayin fitsararriya a fim, inda ta bayyana cewa ta fuskanci masoyanta suna matukar son su ganta a wannan fannin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng