Allah ya isa: Bayan shafe shekaru 6 muna soyayya, kawai sai nake ganin katin aurenshi da wata - Wata budurwa ta koka

Allah ya isa: Bayan shafe shekaru 6 muna soyayya, kawai sai nake ganin katin aurenshi da wata - Wata budurwa ta koka

- Wata budurwa mai suna Khadija Abdullahi ta shiga shafin Twitter ta koka akan yaudararta da saurayinta yayi

- Ta bayyana cewa ta shafe shekaru 6 tana tare dashi, kwatsam sai take ganin katin daurin aurensa a shafin Instagram da wata budurwar

- Ta bayyana cewa baza ta taba yafe mishi ba, tunda ya bata mata shekaru 6 yana yaudararta

Wata budurwa ta koka a shafin sada zumunta na Twitter bayan saurayin da take soyayya da shi na tsawon shekaru 6 ya fara shirye-shiryen auren wata budurwar ba tare da saninta ba.

Budurwar mai suna Khadija Abdullahi ta bayyana cewa bata da masaniya cewa saurayin nata yana shirin aure har sai da ta ga katin auren shi a shafin sada zumunta na Instagram. Ta kara da cewa saboda baya so ta sani har rufeta yayi a manhajar Whatsapp.

KU KARANTA: Rukayya Dawayya: Ban cancanci irin sakin da mijina yayi mini ba, saboda ina da matukar kyau da daukar hankalin namiji

Ga abinda budurwar ta wallafa:

"Na shafe shekaru 6 a banza kan wannan dan iskan, kawai sai nake ganin katin auren shi a shafin Instagram. Wai zai yi aure ranar 14 ga watan July.

"Yanzu dai ya rufe ni a WhatsApp cikin gaggawa, kuma nima na rufe shi. Maza basu da amana ko kadan. Allah ya isa tsakanina da kai."

Da yawa daga cikin abokananta na shafin Twitter suna bata baki akan tayi hakuri Allah zai maida mata da mafi alkhairi, inda suka dinga yin Allah wadai da halin wannan saurayi nata.

Allah dai ya kyauta, yadda labarin Khadija da saurayinta da ya yaudareta ya kasance kenan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng