Babu dalibin da zai kara yin rijista da mu idan bashi da lambar NIN - JAMB
Hukumar tsara jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta ce daga yanzu babu wani dalibi da zai kara yin rijista domin zana jarrabawar ta ba tare da ya mallaki lambar tantance 'yan kasa ba (NIN).
JAMB ta ce wannan sabon tsari zai fara aiki ne daga shekara mai zuwa, 2020.
Shugaban sashen yada labarai na hukumar JAMB, Dakta Fabian Benjamin, ne ya sanar da hakan yayin hutun karshen mako, ya ce daliban da hukumar bayar da katin shaidar dan kasa ta bawa lambar tantance wa (NIN) ne kadai za su iya yin rijista domin rubuta jarrabawar JAMB.
Ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke gabatar da jawabi a wurin wani taron kara wa juna ilimi da hukumar tsara jarrabar kammala makarantar sakandire (NECO) ta shirya a garin Keffi, jihar Nasarawa.
DUBA WANNAN: Ribar da yankin arewa ya samu a karkashi mulkin Buhari
Mista Benjamin ya ce hukumar JAMB ta kammala shiri da hukumar bayar da katin dan kasa (NIMC) domin tabbatar da sabon tsarin ya fara aiki a shekara mai zuwa.
Ya ce yin hakan na daga cikin kokarin hukumar JAMB na dakile makudin jarrabawa ta hanyar sojan gona da musayar bayanan masu rubuta jarrabawa.
Da ya ke magana a wurin taron, darekta a hukumar NECO, Mustapha Abdul, ya bayyana cewar kaso 50% na magudin jarraba wa da ake tafka wa na ya na faruwa ne lokacin rijistar dalibai.
Kazalika, ya amince da matakin hukumar JAMB na yin amfani da lambar tantance wa ta NIN yayin rijistar daliban da zasu zauna jarrabawar UTME.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng