Buhari ya sauka daga kujerar shugabancin kungiyar ECOWAS
Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS sun zabi shugaban kasar jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou, a matsayin sabon shugaba da zai jagoranci kungiyar na tsawon zango guda mai wa'adin shekara daya.
An zabi Issoufou ne yayin taron shugabannin kasashen ECOWAS karo na 55 da aka yi ranar Asabar a Abuja. Sabon shugaban ya karbi jagorancin kungiyar ne daga hannun shugaba Buhari.
A wata sanarwa da babban sakatare a ma'aikatar harkokin kasashen waje, Mustapha Suleiman, ya karanta, ya ce shugabannin sun yaba wa Buhari bisa rawar da ya taka wajen hada kan kasashen da ke zaman mamba a kungiyar ECOWAS.
Kazalika, kungiyar ECOWAS ta amince da sake yin taron ta na gaba a ranar 21 ga watan Disamba na shekarar nan.
Daga cikin shugabannin kasashe 15 da kungiyar ECOWAS ke da su, shugabannin kasashe 13 sun harci taron da aka yi a Abuja.
DUBA WANNAN: Jihohin arewa 7 da aka fi kashe mutane a watan Mayu
Kasashe 13 da shugabanninsu su ka halarci taron su ne; Benin, Burkin Faso, Cote d'Ivoire, Gambia, Ghana, Guinea, Guinea Bissau, Liberia, Mali, Nijar, Najeriya, Sierra Leone, da Togo.
Ministan harkokin waje, Julio Cesar Lopez, ne ya wakilci kasar Cabo Verde, yayin da minsitan harkokin kasashen waje, Amadou Ba, ya wakilci kasar Senegal.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban kotun ICC, Jastis Chile Eboe-Osuji, wakili na musamman a Afrika ta yamma da Sahel daga ofishin shugaban majalisar dinkin duniya da sauran su.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng